Fayemi na shirin barin Majalisar shugaba Buhari

Fayemi na shirin barin Majalisar shugaba Buhari

A yayin da hausawa ke cewa shawara ta rage ga mai shiga rijiya, a yau ne ake sa ran Ministan tattalin ma'adanan kasa, Kayode Fayemi, zai yi murabus daga kujerar sa ta majalisar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wannan lamari yazo ne sakamakon lashe zaben fitar da dan takarar gwamna na jam'iyyar APC da Ministan yayi wanda aka gudanar a ranar 14 ga watan Yuli a jihar Ekiti.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne Ministan ya shaidawa manema labarai na fadar shugaban kasa cewa zai yi murabus daga kujerar sa nan da zuwa mako guda.

Kayode Fayemi

Kayode Fayemi

Wata majiyar rahoto daga fadar shugaban kasa da ta shaidawa shafin jaridar Daily Trust ta bayyana cewa, akwai yiwuwar ministan ya bayyana murabus din sa yayin zaman majalisa na yau laraba da shugaba Buhari ya jagoranta.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya caccaki tsohon Shugaban Kasa Obasanjo akan rashin Wutar Lantarki

Majiyar ta kuma bayyana cewa, ba bu lallai murabus din Ministan ya kawo sauye-sauye cikin majalisar ta shugaba Buhari, inda ake sa ran aikin zai koma ga hannun karamin ministan na ma'aikatar ta tattalin ma'adanan kasa, Mista Bawa Bwari domin ci gaba da gudanar da ita.

Rahotanni sun bayyana cewa, hakan zai bayu ne sakamakon makamancin abinda ya faru yayin da Minista ta kewaye, Amina Muhammad, ta yi murabus domin karbar aikin Sakatariya ta majalisar dinkin duniya, inda karamin ministan ma'aikatar, Ibrahim Jibrin, ya ci gaba da gudanar da al'umman ma'aikatar ba tare da wani sauyi ba daga shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel