Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi sababbin nade-nade guda 5

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi sababbin nade-nade guda 5

- Shugaba Muhammadu Buhari ya sake bayar da wasu sababbin mukamai 5, a cikin wata takarda da ya rubutawa majalisa a ranar 23 ga watan Mayu

- Shugaban kasar ya bukaci majalisar da ta tantance masa da mutanen biyar a matsayin Daraktoci na kungiyar babban bankin Najeriya (CBN)

- Majalisar tayi la’akari da bukatar shugaban kasar na tantance wadanda yakeso ya nada su biyar a matsayin Daraktocin babban bankin Najeriya a cikin tsari

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake bayar da wasu sababbin mukamai 5, a cikin wata takarda da ya rubutawa majalisa a ranar 23 ga watan Mayu.

Shugaban kasar ya bukaci majalisar da ta tantance masa mutanen biyar a matsayin Daraktoci na kungiyar babban bankin Najeriya (CBN).

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi sababbin nade-nade guda 5

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi sababbin nade-nade guda 5

Majalisar tayi la’akari da bukatar shugaban kasar na tantance wadanda yake so ya nada su biyar a matsayin Daraktocin babban bankin Najeriya a cikin tsari.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An sake garkuwa da fasinjoji 42 a Birnin-Gwari zuwa Kaduna

Mutanen sune:

1. Farfesa Ummu Ahmed Jalingo- Arewa maso gabas

2. Farfesa Justina Odinakachukwu Nnabuko- Kudu maso Gabas

3. Farfesa Mike I. Obadan- kudu maso Kudu

4. Dr. Abdu Abubakar- Arewa maso Yamma

5. Adeola Adetunji- Kudu maso Yamma

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel