‘Yan majalisar jihar Ondo sun ba hammata iska kan mayar da mataimakin shugaban majalisar da aka sauke

‘Yan majalisar jihar Ondo sun ba hammata iska kan mayar da mataimakin shugaban majalisar da aka sauke

- Tashin hankali ya baibaye majalisar jihar Ondo a jiya sakamakon ‘yan majalisar da sukayi doke doke akan umurnin da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu ya bayar na mayar da mataimakin shugaban majalisar da aka cire

- Sakamakon rikicin manyan jami’an tsaro na jihar suka garzaya zuwa majalisar domin kwamtar da rikicin wanda ‘yan majalisar ke tayi a kusa da ofishin shugaban majalisar Bamidele Oleyelogun

- Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Gbenga Adeyanju dana ‘yan sanda masu farin kaya (DSS) tare da wasu jami’an tsaro na jihar sun garzaya majalisar domin kawo zaman lafiya

Tashin hankali ya baibaye majalisar jihar Ondo a jiya sakamakon ‘yan majalisar da sukayi doke doke akan umurnin da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu ya bayar na mayar da mataimakin shugaban majalisar da aka cire.

Sakamakon rikicin manyan jami’an tsaro na jihar suka garzaya zuwa majalisar domin kwamtar da rikicin wanda ‘yan majalisar ke tayi a kusa da ofishin shugaban majalisar Bamidele Oleyelogun.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Gbenga Adeyanju dana ‘yan sanda masu farin kaya (DSS) tare da wasu jami’an tsaro na jihar sun garzaya majalisar domin kawo zaman lafiya.

‘Yan majalisar jihar Ondo sun ba hammata iska kan mayar da mataimakin shugaban majalisar da aka sauke

‘Yan majalisar jihar Ondo sun ba hammata iska kan mayar da mataimakin shugaban majalisar da aka sauke

Ciyaman na jam’iyyar tasu Ade Adetimehin, ya isa majalisar domin magana da ‘yan majalisar, wanda rikicin ya samo asali ne sakamakon gwamnan jihar da ya bayar da umurnin a gaggauta mayar da mataimakin shugaban majalisar da aka sauke, hakan yayi sanadiyyar rarrabuwar kawunan ‘yan majalisar.

KU KAANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Daura da Olanisakin sun isa majalisar dattawa domin korowa yan majalisan bayanai akan kashe-kashe

12 daga cikin ‘yan majalisar a shirye suke da su mayar da mataimakin shugaban majalisar sai kuma 14 daga ciki suka tubure akan cewa an kore shi saboda haka babu maganar dawo dashi, kamar yanda majiyarmu ta ruwaito cewa gwamnan ya gana da su ne a ranar Talata, game da lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel