Yanzu Yanzu: Daura da Olanisakin sun isa majalisar dattawa domin korowa yan majalisan bayanai akan kashe-kashe

Yanzu Yanzu: Daura da Olanisakin sun isa majalisar dattawa domin korowa yan majalisan bayanai akan kashe-kashe

Shugaban hukumar DSS, Lawan Daura tare da shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Abayomi Olonisakin, sun isa majalisar dattawa domin yin jawabi ga yan majalisa kan lamarin tsaro a kasar.

Yayinda Olonisakin ya fara isa wajen, Daura ya isa waje da misalin karfe 11:25 na safe.

Su duka biyun na jira a ofishin babban maiba shugaban majalisar dattawa shawara akan lamuran majalisa, Sanata Ita Enang kafin a kirasu zauren majalisar domin jawabin.

Majalisa ta aika sammaci ga shugabannin tsaro da hukumomin tsaro a kasar, ciki harda hukumar kula da shige da fice na Najeriya, domin koro jawabai ga yan majalisa.

KU KARANTA KUMA: Ana rikici akan kujerun ‘yan majalisa da suka rasu akan mulki

An tattaro cewa baya ga Daura da Olonisakin, dukannin sauran hukumomin sun turo wakilansu ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel