Rikicin Boko Haram ya jefa rayuwar Mutane Miliyan 14.8 cikin mawuyacin hali

Rikicin Boko Haram ya jefa rayuwar Mutane Miliyan 14.8 cikin mawuyacin hali

- An shafe kimanin shekaru 9 da fara rikicn Boko Haram

- Kuma rikicin ya tilastawa Miliyoyin Mutane barin gidajensu da dukiyarsu domin tsira da rayukansu

- Amma Gwamnatin Najeriya ta bayyana irin kokarin da take yi wajen ganin ta kawo karshensa

Najeriya ta bayyana cewa kimanin kusan mayakan Boko Haram 700 suke da niyyar mika wuya a rikicin da ake cigaba da fafatawa tun shekaru tara da suka wuce a yankin Arewa masu tsakiyar kasar.

Rikicin Boko Haram ya jefa rayuwar Mutane Miliyan 14.8 cikin mawuyacin hali

Rikicin Boko Haram ya jefa rayuwar Mutane Miliyan 14.8 cikin mawuyacin hali

Jakadan Najeriya a Majalisar dinkin Duniya Farfesa Tijjani Bande ne ya bayyana cewa kimanin Mutane Miliyan 14.8m rikicin ya rutsa da su kuma Mutane Miliyan 1.7m ne suka zama ‘yan gudun hijira a sakamokon rikicin wanda mafi yawancinsu Mata ne da kananan yara ga kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Daura da Olanisakin sun isa majalisar dattawa domin korowa yan majalisan bayanai akan kashe-kashe

Da yake magana Farfesa Bande yayin da Majalisar take tattauna kan batun kare hakkin farar hula a yayin rikici da muggan makamai. Ya bayar da tabbacin cigaba da rage radadin matsanancin halin da rikicin na Boko Haram ya jefa Muta

Rikicin Boko Haram ya jefa rayuwar Mutane Miliyan 14.8 cikin mawuyacin hali

Rikicin Boko Haram ya jefa rayuwar Mutane Miliyan 14.8 cikin mawuyacin hali

"A halin yanzu muna cigaba da hadin gwuiwa da kasashen da ke da iyaka da mu kamar kasar Chad, Cameroon, Benin da kuma kasar Niger domin dakele duk wani yunkuri na 'yan tada kayar bayan na Boko Haram, musamman dan tabbatar da tsaro ga mata da kuma kananan yara a yankin."

Rikicin Boko Haram ya jefa rayuwar Mutane Miliyan 14.8 cikin mawuyacin hali

Rikicin Boko Haram ya jefa rayuwar Mutane Miliyan 14.8 cikin mawuyacin hali

Ya cigaba da cewa Najeriya ita ce kasa ta farko da zata fara kawo tsaro a makarantun kasar, kama daga firamari har zuwa manyan makarantu domin samun ingantaccen tsaro da zaman lafiya. Ya ce tsarin yana daga cikin kudurin gwamnatin Tarraya tun a shekara ta 2014 akan harkokin da suka shafi tsaro.

Ya cigaba da bayyana cewa "Tabbas abin bakin ciki ne da bacin rai idan aka yi duba da irin mata da kananan yara da ake sacewa a sanadin wannan rikici, amma a yanzu gwamnatin Najeriya ta yi nasarar dakile duk wani yunkuri mai kama da hakan."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel