Na annabi basu karewa: Maishara a filin jirgin sama ta mayar da $6,000 da ta tsinta a bayi

Na annabi basu karewa: Maishara a filin jirgin sama ta mayar da $6,000 da ta tsinta a bayi

A daidai lokacin da wasu suke bata sunan Najeriya a idon mutan kasar wajen ta hanyar rashawa da cin hani, wata ma’aikaciya mai shara a babban filin jirgin saman Murtala Muhammed International Airport (MMIA), Ikeja, Legas ta yi abin a zo a gani.

Ma’aikaciyar mai suna Charity Bassey, ta ga jakan kunshe da kudin dalarAmurka $6000, wato kimanin N2million a kundin Najeriya, amma ta mayarwa jami’an tsaro domin suyi cigiya, a nemi mai kudin.

Maihsaran wacce ta ke aiki karkashin kamfanin Lakewood Development Company, nab akin aikinta ne kawai sai wani fasinja ya fada mata akwai wani abu a cikin bayin.

KU KARANTA: Har yanzu ba Mu kai ga kama wanda ya sace Sandar Majalisa ba - ‘Yan sanda

Tace: “Na shiga ciki nag a wani karamin bakin leda a kasa. Ba zaka san kudi ke ciki ba. Sai na dauka, nag a alamun kudi ne a ciki sannan na kaiwa masu kula da kwastomomi. Da na kirga kudin, nag a kudi $100 guda 60 a cikin.”

Da aka tambayeta me take son a bata a matsayin ladan wannan kyakkyawan dabi’a da ta nuna, tace ba komai. “Babu wanda ya bani wani abu, ko mai kudin da ya dawo daga baya bai bani komai ba, har da kamfanin. Amma ko a jikina, ba zan gushe ina aiki da gaskiya ba. Wannan bas hi bane lokacin farko da zan tsinci lalita, wayar salula, jakunkuna ko kudi ba kuma mayar da su nike yi,”

Za ku tuna cewa a shekarar 2014, wata ma’aikaciyar filin jirgin sama, Josephine Agwu, ta tsinci 12 million a cikin bayi amma ta mayar, daga baya aka bata kyaututtuka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel