Majalisa ta harzuka bayan ‘yan Sanda sun ce bincike akan satar sandar girma zai iya daukar shekara 10

Majalisa ta harzuka bayan ‘yan Sanda sun ce bincike akan satar sandar girma zai iya daukar shekara 10

- Kwamitin majalisa wanda ke bincike akan shigar da akayi majalisa sun yi korafi akan bata lokaci da ‘yan sanda keyi wurin karasa bincike akan lamarin fiya da wata daya bayan faruwar lamarin

- Kwamitin majalisun biyu wanda Sanata Bala Ibn Na-Allah (APC, Kebbi) da kuma Rep Betty Apiafi (PDP, Rivers), ta sanar da haka, a lokacin da kwamishinan ‘yan sanda mai kula da harkokin IG Abu Sani ya tsaya a gabanta

- ‘Yan ta’adda a kalla biyar a ranar 18, ga watan Afirilu, na wannan shekarar suka shiga majalisar suka saci sandar girma wanda shine alamun doka a majalisar

Kwamitin majalisa wanda ke bincike akan shigar da akayi majalisa sun yi korafi akan bata lokaci da ‘yan sanda keyi wurin karasa bincike akan lamarin fiya da wata daya bayan faruwar lamarin.

Kwamitin majalisun biyu wanda Sanata Bala Ibn Na-Allah (APC, Kebbi) da kuma Rep Betty Apiafi (PDP, Rivers), ta sanar da haka, a lokacin da kwamishinan ‘yan sanda mai kula da harkokin IG Abu Sani ya tsaya a gabanta.

‘Yan ta’adda a kalla biyar a ranar 18, ga watan Afirilu, na wannan shekarar suka shiga majalisar suka saci sandar girma wanda shine alamun doka a majalisar.

Majalisa ta harzuka bayan ‘yan Sanda sun ce bincike akan satar sandar girma zai iya daukar shekara 10

Majalisa ta harzuka bayan ‘yan Sanda sun ce bincike akan satar sandar girma zai iya daukar shekara 10

Sani ya fadawa kwamitin bincike akan lamarin cewa baza’a iya gama shi ba sannan kuma ya tabbatarwa kwamitin cewa suna iyakar kokarinsu don gano musabbabin aukuwar al’amarin, duk da cewa wadanda aka kama da hannun a cikin lamarin sun karyata cewar hannu a ciki.

KU KARANTA KUMA: Ana rikici akan kujerun ‘yan majalisa da suka rasu akan mulki

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Omo-agege ya ki cewa uffan kan tuhumar da ake masa a gaban kwamitin bincike akan satar sandar iko, inda yace amsa wata tambaya kamar daure kaine domin ya shigar da kara kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel