Kungiyar CAN ta mika kokon bara wurin gwamnatin Najeriya a kan batun jakadanci

Kungiyar CAN ta mika kokon bara wurin gwamnatin Najeriya a kan batun jakadanci

Kungiyar kiristoci ta Najeriya ta bukaci gwamnati da ta mayar da ofishin tan a jakadanci dake kasar Isra’ila daga birnin Tel Avi zuwa Jerusalem.

Shugaban kungiyar CAN, Dakta Samson Ayokunle, ne ya yi wannan kira a cikin wata takarda da mai magana da yawun sa, Adebayo Oladeji, ya fitar jiya a Abuja.

Kungiyar CAN ta mika kokon bara wurin gwamnatin Najeriya a kan batun jakadanci

Kungiyar CAN ta mika kokon bara wurin gwamnatin Najeriya a kan batun jakadanci

Ayokunle ya mika sakon taya murna ga kasar Isra’ila a yayin da suke murnar cika shekaru 70 a matsayin kasa tare da bayyana cewar mayar da ofishin jakadancin zuwa Jerusalem zai zama tamkar wata hanya ce da Najeriya zata taya kasar murnar wannan bikin da take yi.

KU KARANTA: Buhari ya kalubalanci Obasanjo a kan kashe $16bn a fanin wutan lantarki

A cewar sa, bayyana Jerusalem a matsayin shelkwatar birnin Isra’ila da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi a watan Disambar bara, cikar alkawarin ubangiji ne kamar yadda yake a cikin littafin Injila.

Kazalika ya jinjinawa Trump da kasar Amurka a kan kokarin su wajen ganin birnin Jerusalem ya koma hannun mabiya Kirista..

Muna murna wasu kasashen Duniya da suka hada da Amurka, Romania, Paraguay da sauran su sun mayar da ofishin jakadancin su Jerusalem. Muna jiran gwamnatin Najeriya zata bi sahun kasashen Duniya ta hanyar mayar da ofishin jakadancin ta Jerusalem,” inji Dakta Ayokunle.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel