Wata mai shara a filin tashin jirage ta tsinci $6000, ta dawo da su

Wata mai shara a filin tashin jirage ta tsinci $6000, ta dawo da su

A wannan lokaci da ake ta bankado badakalar cin hanci da rashawa a fanoni daban-daban a Najeriya, wata mai aikin kwashe shara a filin tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas, Charity Bassey bawa mutane mamaki yayinda ta tsinci $6,000 amma ta mayar dashi zuwa ga mahukuntar filin jirgin.

Matar tana aiki ne da kamfanin Lakewood development Company wanda suka shahara wajen ayyukan shara da goge wurare. A cewarta, tana tsaye a kofar wani ban daki ne wani fasinja ya janyo hankalinta inda ya ce akwai wani bakin leda a cikin ban-dakin.

Wata mai shara a filin tashin jirage ta tsinci $6000, ta dawo da su

Wata mai shara a filin tashin jirage ta tsinci $6000, ta dawo da su

KU KARANTA: Wani saurayi ya kashe budurwar sa, ya cusa gawar ta cikin kwandon shara

"Na shiga cikin ban-dakin inda naga leda a kasa. Ledan ya yi kura sosai babu wanda zaiyi tsamanin akwai kudi a cikinsa. Na dauki ledan kuma sai na ji alamu kamar kudi ne a ciki. Daga nan zai na garzaya wajen jami'ai masu sauraron koken mutane inda aka bani safar hannu kuma na bude ledan na kirga $100 guda 60."

Yayin da aka tambaye ta ko anyi mata wani tukwuici saboda halin gaskiya da ta nuna, sai ta ce "Babu wanda ya bani komai, har ma manajan filin jiragen saman da shugaban kamfanin da ta ke yiwa aiki. Amma ni wannan ba matsala bace, hankalina ya kwanta saboda ban ci hakkin kowa ba koma zan cigaba da aiki na kamar yadda ya kamata."

Bassey ta kara da cewa wannan ba shine karo na farko da ta ke tsintuwar kudade, jakuna, wayoyi da sauransu kuma ta mayar wa hukumar filin jiragen samar ba.

A bangarensa, shugaban kamfanin tsaftace muhallin, Sam Nchezor ya ce kamfanin tayi muran da alfahari da halin gaskiya da rikon amana da Bassey ta nuna, ya kuma ce kamfanin tana da niyyar bawa Charity wani tukwuci.

"Zamu bata tukwuici kuma zamu kara mata albashi. Ya kuma rage da hukumar kula da filayen jiragen sama (FAAN) tayi mata wani abin alkhairi. Muna alfahari da ita," kamar yadda ya shaidawa jaridar Guardian.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel