PDP ta mutu kurmus a jihar Kaduna – Uba Sani

PDP ta mutu kurmus a jihar Kaduna – Uba Sani

- Mai bawa gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufa’i shawara ta fannin siyasa, Alhaji Uba Sani, yace zaben da ya gabata da aka gudanar na kananan hukumomi a jihar ya tabbatar da cewa PDP ta mutu

- Sani wanda ‘yan jam’iyyar ta PDP suka zarga da shirya magudin zabe a zaben kananan hukumomi da aka gudanar kwanan nan inda jam’iyyar APC ta lashe, yace dama PDP bazata ci zabe ba sai dai idan ba zaben gaskiya da adalci akayi ba

- Sani yace jam’iyya mai mulki nada adalci tinda har ta bari jam’iyyar adawa taci kujeru hudu na kananan hukumomi a cikin wadanda hukumar zabe ta sanar

Mai bawa gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufa’I shawara ta fannin siyasa, Alhaji Uba Sani, yace zaben da ya gabata da aka gudanar na kananan hukumomi a jihar ya tabbatar da cewa PDP ta mutu.

Sani wanda ‘yan jam’iyyar ta PDP suka zarga da shirya magudin zabe a zaben kananan hukumomi da aka gudanar kwanan nan inda jam’iyyar APC ta lashe, yace dama PDP bazata ci zabe ba sai dai idan ba zaben gaskiya da adalci akayi ba.

Sani yace jam’iyya mai mulki nada adalci tinda har ta bari jam’iyyar adawa taci kujeru hudu na kananan hukumomi a cikin wadanda hukumar zabe ta sanar.

PDP ta mutu kurmus a jihar Kaduna – Uba Sani

PDP ta mutu kurmus a jihar Kaduna – Uba Sani

Ya kara da cewa inda gwamnatin APC ta shirya yin magudi a zaben ne da sunyi yanda sauran jihohi suka yi, shine amfani da hanyar zabe ta da ba tare da tantancewa ba.

KU KARANTA KUMA: Ana rikici akan kujerun ‘yan majalisa da suka rasu akan mulki

A halin da ake ciki ana cigaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnan jihar Kaduna da sanatocin jihar uku dake wakiltan yankunan jihar a majalisar wakilai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel