Ana rikici akan kujerun ‘yan majalisa da suka rasu akan mulki

Ana rikici akan kujerun ‘yan majalisa da suka rasu akan mulki

-Mazabun ‘yan majalisa wadanda suka rasu sun koka akan cewa shugaban majalisar Bukola Saraki da Yakubu Dogara, sunki bayar da dama ga hukumar zabe akan ta gudanar da zaben maye gurbin wadanda suka rasu cikin ‘yan majalisar

-Sanatocin wadanda suka rasu sune Ali Wakili (APC, Bauchi ta kudu), Mustapha Bukar (APC, yankin Daura) sai kuma dan majalisar wakilai Buba Jibril (APC, mazabar tarayyar Lokoja)

-Mutane sun bukaci shuwagabannin majalisun dasu ajiye siyasa a gefe suyi abunda ya dace na bayar da dama a sake zabar wasu daga wadannan mazabobi da suka rasa wakilansu

Mazabun ‘yan majalisa wadanda suka rasu sun koka akan cewa shugaban majalisar Bukola Saraki da Yakubu Dogara, sunki bayar da dama ga hukumar zabe akan ta gudanar da zaben maye gurbin wadanda suka rasu cikin ‘yan majalisar.

Sanatocin wadanda suka rasu sune Ali Wakili (APC, Bauchi ta kudu), Mustapha Bukar (APC, yankin Daura) sai kuma dan majalisar wakilai Buba Jibril (APC, mazabar tarayyar Lokoja).

Mutane sun bukaci shuwagabannin majalisun dasu ajiye siyasa a gefe suyi abunda ya dace na bayar da dama a sake zabar wasu daga wadannan mazabobi da suka rasa wakilansu.

Ana rikici akan kujerun ‘yan majalisa da suka rasu akan mulki

Ana rikici akan kujerun ‘yan majalisa da suka rasu akan mulki

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC zata iya gudanar da zaben maye gurbin wadanda suka rasa rayukansu a majalisar cikin kwanaki 90, tare da sanarwar majalisar; gashi majalisar tayi shuru akan lamarin saboda haka kujerun zasu kasance babu kowa a kansu.

Jagorori daga mazabobin ‘yan majalisun sunyi korafi akan cewa ya kamata shuwagannin majalisun su sanar da INEC cewa ta gudanar da zaben maye gurbi ga ‘yan majalisun da suka rasu, domin basa jin dadi ace basu da wakili a majalaisa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel