Rashin tsaro: Shirun Buhari na nufin shanu ya fi ni daraja - Cardinal Okogie

Rashin tsaro: Shirun Buhari na nufin shanu ya fi ni daraja - Cardinal Okogie

- Babban limamin coci na jihar Legas, Anthony Cardinal Okogie, ya fadawa shugaba Muhammadu Buhari, cewa ‘yan Najeriya sun gaji da kisan da akeyi a fadin kasar

- Okogie ya bayyana cewa shiru da shugaba Muhammadu Buhari yayi akan kisan da akeyi a kasar na nuna cewa shanu sun fi mutum daraja

- Okogie yayi gargadin ne hadi da zanga-zangar lumana da addu’o’i da mabiya darikar Katolika suka gudanar a kasar

Babban limamin coci na jihar Legas, Anthony Cardinal Okogie, ya fadawa shugaba Muhammadu Buhari, cewa ‘yan Najeriya sun gaji da kisan da akeyi a fadin kasar.

Okogie ya bayyana cewa shiru da shugaba Muhammadu Buhari yayi akan kisan da akeyi a kasar na nuna cewa shanu sun fi mutum daraja.

Okogie yayi gargadin ne hadi da zanga-zangar lumana da addu’o’i da mabiya darikar Katolika suka gudanar a kasar a jiya.

Rashin tsaro: Shirun Buhari na nufin shanu ya fi ni daraja - Cardinal Okogie

Rashin tsaro: Shirun Buhari na nufin shanu ya fi ni daraja - Cardinal Okogie

Yace zanga-zangar amfaninta shine domin a farfado da shugaban kasa idan ma bacci yake ya tashi don ya dauki mataki akan kisan da akeyi.

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC za ta gurfanar da Shekarau da Wali a ranar Alhamis

Okogie ya nuna rashin jin dadinsa game da halayyar da shugaban kasa ke nunawa akan kisan da ake tayi a fadin kasar nan, yace abun yana nema ya wuce gona da iri a fadin kasar.

Idan bazaku manta ba a jiya ne mabiya darikar Katolika suka gudanar da zanga-zangar lumana a fadin jihohi dake kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel