Wani saurayi ya kashe budurwar sa, ya cusa gawar ta cikin kwandon shara

Wani saurayi ya kashe budurwar sa, ya cusa gawar ta cikin kwandon shara

Yan sanda sun cafke wani mai sayar da kayayakin mota a Legas mai suna Isiah Chukwu wanda ake zargi da aikata kisar gilla ga masoyiyarsa mai suna Joy.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Chukwu da Joy yan asalin jihar Ebonyi ne kuma sun kwashe a kalla shekaru biyu suna zaune tare duk da cewa ba'a daura musu aure ba.

Ana zargin Chukwu da ke zaune a Ladipo da laifin kashe budurwarsa mai shekaru 26 a gidansu da ke Balogun Street a Oshodi kuma ya kulle gawar cikin buhu kuma ya yi nufin ya kai gawar bola.

An damke wani dan kasuwa da ya kashe budursa, ya kuma sanya gawarta a bola

An damke wani dan kasuwa da ya kashe budursa, ya kuma sanya gawarta a bola

KU KARANTA: Buhari ya yabi Abacha, ya ce duk abinda za a fada a kan sa, ya yi rawar gani

Wasu matasa ne sukayi kacibus da Chukwu misalin karfe 4 na asuba yayin da yake janye da gawar a cikin buhu a hanyarsa na zuwa bola, matasan basu gamsu da abinda ke cikin buhun ba kuma suka umurce shi ya bude amma ya yi burus da su.

Wani lamami da ke hanyarsa ta zuwa masallaci ne ya shiga tsakanin Chukwu da matasan inda ya bude buhun kuma ya gano gawa ce a ciki har ma ta fara wari, hakan yasa matasan zukayi masa dukkan tsiya kafin daga bayan yan sanda suka zo suka tafi dashi.

Jami'in hulda da mutane na hukumar Yan sandan jihar, SP Chike Oti ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce za su mika binciken ga sashin binciken manyan laifuka (CID) da ke Yaba.

"Mutumin yana tsare a halin yanzu kuma an mika gawar zuwa inda ake ajiyar gawa a asibiti don gudanar da bincike," inji shi.

Bayan da aka tsananta bincike, Chukwu ya ce ya yi tafiya ne don hallartar jana'iza a Abraka amma da ya kira wayar budurwarsa sai wani na miji ya amsa wayar har ya ke yi masa barazana cewa ya dena damun matarsa.

An gano wuka da ake zargin ya yi amfani dashi wajen kashe budursa tare da wayoyin salula guda hudu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel