Matasan Najeriya sun hurowa Shugaba Buhari wuta a ba su damar takara a 2019

Matasan Najeriya sun hurowa Shugaba Buhari wuta a ba su damar takara a 2019

- Shugaban kasa Buhari ya rage ya sa hannu a kan kudirin rage shekarun takara

- Da zarar kudirin ya zama doka har ‘Dan shekara 35 zai iya zama Shugaban kasa

- Haka kuma masu shekara 25 za su iya takarar kujerar ‘Dan Majalisa a Najeriya

A makon nan ne mu ka samu labari daga Daily Trust cewa kungiyoyi da dama da ke lemar “Not Too Young To Run” sun nemi ayi maza a sa hannu kan kudurin da ya rage shekarun ‘Yan takara a Najeriya.

Matasan Najeriya sun hurowa Shugaba Buhari wuta a ba su damar takara a 2019

Ana nema a sa hannu kan dokar da za ta ba Matasa damar siyasa

Kwanaki Majalisa ta kawo kudirin da zai ba Matasa damar tsayawa takarar kujerun siyasa a kasar kuma yanzu an yi na’am da wannan kudiri. Abin da ake jira kawai shi ne Shugaban kasa Buhari ya rattaba hannun sa kan kudirin.

KU KARANTA: Shugaban Kwamstam yayi kaca-kaca da masu kukan yunwa

‘Daya daga cikin manyan tafiyar “Not Too Young To Run” wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar YIAGA watau Samson Itodo yayi kira ga Shugaban Kasar ya amince da wannan kudiri lokacin da yayi magana da ‘Yan jarida a Birnin Tarayya Abuja.

Samson Itodo yace Matasan Najeriya sun zura idanu kan Shugaba Buhari domin ganin ya maida wannan kudiri ya zama dokar kasa. Itodo yace za su so nan da karshen watan nan Shugaban kasar ya sa hannu domin Matasa su shigo siyasa.

Matasan kasar dai za su so ace a karshen watan nan Shugaba Buhari yayi abin da ya dace. Idan aka yi hakan dai Matasa masu kananan shekaru sun samu goron Ranar Damukaradiyya a Najeriya kenan. An dai dade ana jiran ganin wannan rana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel