Sake zabar Buhari shine abu mafi sauki – Lai Mohammed

Sake zabar Buhari shine abu mafi sauki – Lai Mohammed

Ministan bayanai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa sake zabar gwamnatin Buhari zai zamo abu mai sauki saboda tayi kuma zata cigaba da isar da alkawaran zabe da ta dauka.

Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 22 ga watan Mayu lokacin da ya kai ziyarar gani da ido na hanyar Ibadan-Ilorin.

Ya bayyana cewa martanin da gwamnatin tarayya ke mayarwa masu suka shine kara kaimi wajen ayyukan cigaba wanda zai amfani al’umma inda ya kara da cewa hakan ne yasa shi da abokan aikinsa suka mayar da hankali wajen gyara lamuran kasar, tare da kai ziyarar gani da ido wajen ayyukan da gwamnati keyi tunda ta hau mulki.

Sake zabar Buhari shine abu mafi sauki – Lai Mohammed

Sake zabar Buhari shine abu mafi sauki – Lai Mohammed

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban hukumar kwastam na Najeriya, Hameed Ali, yace malalatan yan Najeriya kadai ne ke ikirarin kasancewa cikin yunwa a karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Bafarawa ya yi bude baki da limamin Makka, Sheikh Sudais (hotuna)

Ali ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayyana nasarorin wannan gwamnati a harkar noma lokacin day a jagoranci mambobin kungiyar magoya bayan Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

A cewarsa garimar abinci baya fadowa daga sama, don haka dole malalata su ji yunwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel