Malalatan yan Najeriya ne kadai ke yunwa a karkashin Buhari – Shugaban Kwastam

Malalatan yan Najeriya ne kadai ke yunwa a karkashin Buhari – Shugaban Kwastam

A ranar Talata, 22 ga watan Mayu, Shugaban hukumar kwastam na Najeriya, Hameed Ali, yace malalatan yan Najeriya kadai ne ke ikirarin kasancewa cikin yunwa a karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ali ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayyana nasarorin wannan gwamnati a harkar noma lokacin day a jagoranci mambobin kungiyar magoya bayan Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

A cewarsa garimar abinci baya fadowa daga sama, don haka dole malalata su ji yunwa.

Ya fadawa Buhari cewa yan Najeriya na bayan sake tsayawarsa takara a zaben 2019.

Malalatan yan Najeriya ne kadai ke yunwa a karkashin Buhari – Shugaban Kwastam

Malalatan yan Najeriya ne kadai ke yunwa a karkashin Buhari – Shugaban Kwastam

Idan bazaku manta ba a baya Legit.ng ta tattaro cewa shugaban kwastam din ya alakanta shawarar da Buharin ya dauka da jagorantar kasar koda shekarunsa suka ja sama da 70 a matsayin soyayyar da yake yiwa Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Bafarawa ya yi bude baki da limamin Makka, Sheikh Sudais (hotuna)

Yace da ace shine Buhari, ba zai taba daukar irin wannan nauyi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel