Zan yi mai yiwuwa game da rikicin ‘Yan Majalisa da Sufetan ‘Yan Sanda - Shugaba Buhari

Zan yi mai yiwuwa game da rikicin ‘Yan Majalisa da Sufetan ‘Yan Sanda - Shugaba Buhari

- Wasu ‘Yan Majalisa sun gana da Shugaban kasa game da batun IGP

- Shugaban Majalisar yace Sufetan ‘Yan Sanda na neman sa da sharri

- Shugaba Buhari dai ya fadawa Sanatoci zai dauki matakin da ya dace

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da wasu Sanatocin Najeriya jiya fadar Shugaban Kasa inda su ka kawo kuka game da Sufetan ‘Yan Sanda na kasar watau Ibrahim K. Idris.

Zan yi mai yiwuwa game da rikicin ‘Yan Majalisa da Sufetan ‘Yan Sanda - Shugaba Buhari

Wasu ‘Yan Majalisa sun gana da Shugaba Buhari

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya koka da cewa Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Kasar na kokarin jefa cikin wani laifi bai san hawa ba kuma bai san sauka ba don haka ya nemi ‘Yan Majalisa su zauna da Shugaba Buhari.

A jiya dai aka dace Sanatocin su ka tattauna da Shugaban kasa game da batun inda Shugaba Muhammadu Buhari yace zai yi abin da ya dace. Sanata Ahmad Lawan ne ya jagoranci Tawagar kuma yayi magana da ‘Yan jarida.

KU KARANTA: Sanatan APC yayi kaca-kaca da Majalisar Bukola Saraki

Ahmad Lawan ya bayyanawa manema labaran da ke cikin Fadar Shugaban kasa cewa sun ga Shugaba Buhari kuma yayi alkawarin daukar mataki kan lamarin. Wani babban Sanatan Kasar Abdullahi Adamu shi ma dai ya ce wani abu.

Sanata Abdullahi Adamu yace siyasa ce kurum ke nema ta shiga tsakanin Shugaban ‘Yan Sandan Kasar da Shugaban na Majalisar Dattawa. Bukola Saraki na tunani ‘Yan Sanda na neman tursasa wasu masu laifi su kira sunan sa a bincike.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel