Buhari ya yi gaskiyar, Obasanjo ne silar tabarbarewa wuta a Najeriya – Atiku Abubakar

Buhari ya yi gaskiyar, Obasanjo ne silar tabarbarewa wuta a Najeriya – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa tsohon maigidansa, Cif Olusegun Obasanjo ne ummul aba’isun tabarbarewar wutar lantarki a Najeriya, sakamakon wasu matakai marasa karko da ya dauka.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Atiku ya bayyana haka ne a cikin wani hira da yayi da jaridar Punch,inda yace da gangan yaki yarda ya baiwa Obasanjo hadin kai a wata gurguwar kokarin samar da wuta a Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Gombe ta girgiza a sanadiyyar mutuwa da ta rutsa da wani babban jami’inta

Tsohon mataimakin shugaban kasa yace Obasanjo ya yi wa abin diban Karen mahaukaciya ne, wanda a cewarsa ba haka ya dace abi aikin ba, yace kamata yayi abi matsalar daki daki, mataki mataki har zuwa cimma bukata, amma dayake Obasanjo ne shugaba, sai yayi gaban kansa.

Buhari ya yi gaskiyar, Obasanjo ne silar tabarbarewa wuta a Najeriya – Atiku Abubakar

Atiku Abubakar

“Abinda yake ganin ya dace a yi daban, abinda nake ganin ya dace kuma daban, don haka ya bi dama ne, na bi hagu, ya bukaci na zama shugaban kwamitin, amma ban taba zama a kwamitin ba, Ministan wuta, Liyel Imoke na baiwa daman shugabantar kwamiti.

“Na fada masa cewa kamata yayi mubi abin daki daki, mu fara da gyare gyaren wutar lantarkin Najeriya daga bukatun gajerar zango, sai mu dauka daga nan har zuwa dogon zango, amma ya ki ji, ya yi ma lamarin diban karen mahaukaciya, ga shi har yanzu babu wutar.” Inji Atiku.

Atiku yaci gaba da fadin da Obasanjo ya bi ta tashi, da tun a shekarar 2005 Najeriya ta samu isashshen wutar lantarki, saboda tsarin gajeren zango, matsakaicin da kuma dogon zango zai habbaka samar da wutar lantarki a Najeriya.

“Mun samu manyan kamfanoni da suke da nufin zuba jari da ya kai dala miliyan 500, dala miliyan 250 don su kakkafa kananan da matsakaita tashohin wutar lantarki a duk sassan kasar nan, amam Obasanjo yace lallai sai mun yi amfani da iskar Gas, ni kuwa nace masa gyara kuwa ba yau ba.

“Na nusashe shi da cewa akwai tashin tashina a yankin Kudu maso kudu, don haka har sai ka samar da zaman lafiya a yankin sa’annan zaka fara tunanin fitar da iskar gas ta zata samar da wuta, ga batun kera bututun da zasu fitar da Gas wanda hakan zai dauki tsawon lokaci, ko a shekara goma ba za a kammala aikin ba, amma duk da haka yace ya ji ya gani.” Inji Atiku.

Daga karshe Atiku yace da wannan ne yasa a lokacin da majalisar wakilai ta kaddamar da bincike kan zargin kashe dala biliya 16 a harkar wutar lantarki bata gayyace ni ba, saboda bani da hannu cikin duk wata harkalla da aka kull a wancan lokaci.

“An baiwa mutane kwangilar gyaran wutar lantarki, an biyasu kudadensu gaba daya ba a zuwa daya, yan kwangila sun yi batan dabo da kudaden, wasu ma sun saci kudaden, amma duk da haka babu wutar.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel