Sojojin Najeriya sun daka ma yan bindiga wawa sun shekar da 68 a jihar Zamfara

Sojojin Najeriya sun daka ma yan bindiga wawa sun shekar da 68 a jihar Zamfara

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da Dakarun Soji sun hallaka yan bindiga dai dai har guda sittin a takwas, 68, tare da kama masu garkuwa da mutane guda shidda, da kuma kwato babura guda 17, duk a jihar Zamfara.

Kwamandan Birget ta daya dake jihar Sakkwato,Udeagbala Kennedy ne ya bayyana haka a ranar Talata 22 ga watan Mayu, a yayin da yake mika wasu masu garkuwa da mutane su shidda ga kwamishinan Yansandan jihar Zamfara.

KU KARANTA: Zargin ɓarnatar da dala biliyan 16: Babu abinda ka sani – Obasanjo ga Buhari

“Rundunar Sojan kasa tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun kaddamar da aiki na musamman da nufin kakkabe yan bindiga daga jihar, inda dsaga watan Afrilu zuwa Mayu mun kashe yan bindiga guda 68, sai dai kash mun yi asarar jajirtattun Sojoji guda biyu, Kyaftin Muhammad da Kurtu Mijinyawa.

Sojojin Najeriya sun daka ma yan bindiga wawa sun shekar da 68 a jihar Zamfara

Sojoji

“Baya da babura guda goma sha bakwai da muka kwato daga hannun yan bindigar da suka tsere, mun kama wasu guda masu garkuwa da mutane guda shidda, da wani mugun mutumi dake safarar bindigu. Don haka shelkwatar rundunar Sojin kasa ta umarci na mika masu laifin da baburansu ga hukumar Yansanda da hukumar tsaro ta farin kaya don cigaba da bincike.” Inji shi.

A nasa jawabin, kwamishinan Yansandan jihar,Ebrimson ya danganta nasarorin da aka samu ga kyakkyawar alaka dake tsakanin dukkanin hukumomin tsrao dake aikin tabbatar da tsaro a jihar.

Daga karshe kuma ya yi kira ga mazauna yankunan da lamarin ya fi kamari da su taimaka jami’an tsaro da muhimman bayanai don daukan matakan da suka dace.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel