Da ni ne kai da ban nemi Shugabancin Najeriya ba yayin da na haura shekaru 70 - Kanal Hameed ga Shugaba Buhari

Da ni ne kai da ban nemi Shugabancin Najeriya ba yayin da na haura shekaru 70 - Kanal Hameed ga Shugaba Buhari

A ranar Talatar da ta gabata ne Kwanturola Janar na hukumar Kastam, Kanal Hameed Ali mai ritaya, ya shaidawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ra'ayin sa dangane da kasancewar sa shugaban kasa yayin da ya kai shekaru 70 a duniya.

Shugaban na hukumar Kastam ya bayyana cewa, da a ce zai zamto shugaba Buhari to da kuwa bai nemi kasancewa shugaban kasa yana mai shekaru 70 da haihuwa ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Kanal Ali ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci tawagar magoya bayan shugaba Buhari zuwa ziyartar sa gami da ganawa a fadar sa ta Villa dake garin Abuja.

Tawagar Shugaban hukumar Kastam yayin ziyarar shugaba Buhari a Fadar sa

Tawagar Shugaban hukumar Kastam yayin ziyarar shugaba Buhari a Fadar sa

Kwanturola Janar na hukumar kastam din ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya zabi wannan tafarki ne a sakamakon tsantsagwaron kishi gami da soyayya da yake yiwa kasar ta Najeriya.

KARANTA KUMA: Sanata Shehu Sani yayi martani ga Shugaba Buhari akan harin Birnin Gwari

Baya ga haka Kanal Ali ya ci gaba da cewa, a sakamakon nagarta ta adalci, gaskiya da kuma rikon amana da shugaba Buhari ke yiwa kasar nan ya sanya za su marasa baya dari bisa dari a yayin da yake fafutikar sa ta sake neman takarar kujerar shugaban kasa.

Ya kara da cewa, a madadin shugaba Buhari ya nemi ya huta inda zai zaman sa hankali kwance a gidan sa dake Daura, ya gwammace ya jajirce wajen cimma burin sa a kujerar shugaban kasa sakamakon kishi da kuma soyayyarta da ta mamaye zuciyar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel