Gwamnatin tarayya ta bayyana haramtattun makamai, manyan motoci da aka gano a gidan Sambo Dasuki

Gwamnatin tarayya ta bayyana haramtattun makamai, manyan motoci da aka gano a gidan Sambo Dasuki

Gwamnatin tarayya a yau Talata ta bayyanawa babban kotun tarayya da ke zaune a Abuja manyan motoci 11 da muggan makamai da suka gano a gidan tsohon NSA, Sambo Dasuki, a gidansa da ke Abuja a wani farmaki da hukumar DSS ta kai a watan Yulin 2015.

Gwamnatin tarayya ta bayyanawa kotu wadannan abubuwa ta mai bada shaida a kotu, William Obiora, wani jami'in DSS wanda yayi musharaka a farmakin da hukumar ta kai tsakanin ranan 16 da 17 na watan Yuli, 2015.

Lauyan gwamnati ya bayyanawa kotu cewa wasu daga cikin makaman mallakan gwamnati ne amma Dasuki ya sace yayinda ake ofis.

Gwamnatin tarayya ta bayyana haramtattun makamai, manyan motoci da aka gano a gidan Sambo Dasuki

Gwamnatin tarayya ta bayyana haramtattun makamai, manyan motoci da aka gano a gidan Sambo Dasuki

Dasuki ya kasance a garkame a ofishin hukumar DSS tun watan Disanban 2015.

Obiora, wanda ya bada shaida an boye fuskarsa domin bashi kariya. An lissafo abubuwa 29 da aka gano a gidansa.

KU KARANTA: Shirya nike da binciken da Buhari yace zai yi a kaina - Obasanjo

Gwamnatin shugaba Buhari ta ki sakin Kanal Sambo Dasuki duk da cewa kotuna daban-daban sun bada belinsa. Ba da dadewan nan ba, wata kotun ta sake bada belinsa amma hukumar DSS ta ki sakinsa.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Kotun koli ta kasa wadda ake yi wa lakabi da kotun Allah-ya-isa ta yanke hukuncin karshe a game da takaddamar shari'ar da ake ta tafkawa a tsakanin tsohon mai ba sohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara ta fannin tsaro, Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya) da ake cigaba da yi a wani boyayyen wuri na musamman.

Da suke yanke hukuncin, kotun a ta bakin babban alkalin kotun Mai shari'a Ajembi Eko ya bayyana cewa kotun ta kuma gano cewa ba hukumar EFCC ce ba ke dauke da alhakin cigaba da tsare Kanal Dasuki din.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel