Zargin ɓarnatar da dala biliyan 16: Babu abinda ka sani – Obasanjo ga Buhari

Zargin ɓarnatar da dala biliyan 16: Babu abinda ka sani – Obasanjo ga Buhari

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya karyata zargin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi masa na cewa wai gwamnatinsa ta kashe dalan Amurka biliyan 16 don saita wutar lantarkin Najeriya a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, inji rahoton Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne a yayin ganawa da tawagar kungiyar magoya bayan Buhari, BSO, a fadar Aso Rock, inda yace: “Daya daga cikin tsofaffin shuwagabannin kasar nan yana bugun kirji wai ya kashe fiye da dala biliyan 15 a gyaran wuta, shin ina wutar? Kuma ya barmu da biyan bashi.”

KU KARANTA: Karfin shari’a: Wani Mutumi ya yi barazanar kashe makwabcinsa, ya ɗanɗana kuɗarsa

Sai dai Kaakakin Obasanjo Kehinde Akinyemi ya musanta wannan zargi, inda yace Buhari bai san koma game da lamarin, kuma bashi da wata hujja da zata tabbatar da zargin: “Obasanjo ya samu labarin jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, da alama babu abinda ya sani game da wutar Najeriya.

Zargin ɓarnatar da dala biliyan 16: Babu abinda ka sani – Obasanjo ga Buhari

Ga Obasanjo ga Buhari

“Mun tabbata Buhari na maimaita zargin da magajin Obasanjo, Umaru Musa Yar’adua ya yi ma Obasanjo, inda yace majalisar wakilai ta wanke Obasanjo daga wannan zargin, haka nan ma Obasanjo sha musanta wannan zargi a wurare da dama, ciki har da littafinsa, My Watch, inda ya kawo rahotannin binciken EFCC da na kwamitin majalisar wakilai da Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranta, kan adadin kudaden da aka kashe a samar da wutan lantarki, dakon shi da raba shi, daga 199-2007.

“Ina kira ga shugaba Buhari ya karanta shapi na 41, 42, 43 da 47 na littafin ‘My Watch don fahimtar yadda Obasanjo ya bayani filla filla dangane da yadda aka tafiyar da bangaren wutar lantarkin Najeriya. Idan kuma ba zai iya karanta littafin ba mai mujalladi uku, toh ya baiwa hadimansa su karanta masa, kuma su fassara masa ta harshen da zai fi ganewa.” Inji Obasanjo.

Bugu da kari Obasanjo ya bayyana cewa bai taba ikirarin kashe dala biliyan 16 ba a gyaran wutar lantarki, kuma yace Yar’adua ne ya hana shigo da kayan wutar lantarki na cibiyoyi guda bakwai dake fadin Najeriya da kuma na’urarorin samar da wuta masu amfani da iskar gas guda 18, wanda ya manta dasu da gangan a tashoshin jiragen ruwa na Najeriya.

Daga karshe Cif Olusegun Obasanjo ya kalubalanci gwamnatin Buhari da ta kaddamar da kwamitin bincike idan tana tababar rahoton da hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta samar bayan kammala binciken badakalar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel