Wasu kayayyaki 41 ba zasu ci moriyar musayar kudi da kasar China ba

Wasu kayayyaki 41 ba zasu ci moriyar musayar kudi da kasar China ba

Babban bankin Najeriya (CBN) ya fitar da jerin wasu kayayyaki 41 da ba zasu ci moriyar musayar kudade tsakanin gwamnatin Najeriya da ta kasar China ba kamar yadda yake a cikin yarjejeniyar da kasashen suka tsara ba.

Mista Isaac Okafor, mukaddashin daraktan kula da harkokin sadarwa na CBN y ace dokar gwamnatin Najeriya na hana shigowa da wasu kayayyaki na nan daram.

Wani jami’I a cibiyar kasuwanci, masana’antu da ma’adanai a jihar Kano, Malam Attahiru Magaji Gwarzo, y ace akwai amfani a cikin wannan tsari da gwamnati ta zo das hi tare da bayyana cewar sai anyi hakuri sannan za a ci moriyar tsarin.

Wasu kayayyaki 41 ba zasu ci moriyar musayar kudi da kasar China ba

Wasu kayayyaki 41 ba zasu ci moriyar musayar kudi da kasar China ba

Gwarzo ya bayyana cewar hakan zai bunkasa kasuwancin Najeriya day a dogara da kayayyakin da aka shigo das u daga kasashen ketare wadanda kuma yanzu suka yi tashin gwauron zabi saboda tsadar dalar Amurka.

DUBA WANNAN: Magoya bayan Shekarau sun cika harabar hukumar EFCC a jihar Kano

Daga cikin kayayyaki 41 da gwamnatin ta ce ba zasu ci moriyar wannan musayar kudi ba akwai Shinkafa, Kwanon rufi, Tumatirin gwangwani da sauran su.

Gwamnati ta bayyana cewar manufar tsarin ba shine mayar da Najeriya wurin jibge kayayyakin da ake sarrafawa a kasashen ketare ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel