Magoya bayan Shekarau sun mamaye harabar hukumar EFCC a jihar Kano (Hoto)

Magoya bayan Shekarau sun mamaye harabar hukumar EFCC a jihar Kano (Hoto)

Dandazon magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, sun mamaye harabar ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) dake garin Kano.

A yau ne ake saka ran tsohon gwamna Shekarau da Ambasada Aminu Wali zasu bayyana a ofishin hukumar EFCC a cigaba da tuhumar su da badakalar kudin yakin neman zaben 2015.

Magoya bayan Shekarau sun yi Allah wadai da gayyatar gogan nasu tare da bayyana cewar ana yi masa makarkashiya ne irin ta siyasa musamman ganin cewar, har ya kammala wa’adin sa na shekaru 8 a matsayin gwamna ba a same shi da wata almundahana ba.

Magoya bayan Shekarau sun mamaye harabar hukumar EFCC a jihar Kano (Hoto)

Dandazon magoya bayan Shekarau a harabar hukumar EFCC a jihar Kano

Hukumar EFCC na zargin Shekarau da karbar miliyan N25m daga cikin kudin sayen makamai da jam’iyyar PDP tayi amfani da su domin yakin neman zaben shekarar 2015.

Shekarau ya sha musanta zargin cewar ya karbi kudin yakin neman zaben duk da ya amince cewar a gidan sa ne aka kasafta kudin bayan an kawo kason jihar Kano.

DUBA WANNAN: Wani matashi ya zubar da hakoran ubangidan sa da guduma a kan albashin wata 5

Kazalika, Shekarau, ya bayyana cewar ana tuhumar sa ne saboda ya soki gwamnatin shugaba Buhari sannan ya bayyana aniyar sat a neman takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP.

‘Yan Jam’iyyar PDP na yawan kukan cewar hukumar EFCC na yi masu bita da kulli saboda ba a kama ‘ya’yan jam’iyyar APC a duk yaki da cin hanci da gwamnatin ke tutiya da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel