Don kawai na ce Buhari ya gaza shi yasa EFCC ke tuhuma ta da satar kudi – Malam Shekarau

Don kawai na ce Buhari ya gaza shi yasa EFCC ke tuhuma ta da satar kudi – Malam Shekarau

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa tuhumarsa da hukumar yaki da rashawa, EFCC ke yi masa baya rasa nasaba da hirar da ya yi da wata kafar sadarwa, inda yace Buhari ya gaza, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a shekarar 2016 ne hukumar EFCC ta damko wuyar Shekarau game da badakalar naira miliyan dari tara da hamsin, N950m kudin yakin neman zaben tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, inda ta ce ya zaftari nasa Kason daga kudin.

KU KARANTA: Karfin shari’a: Wani Mutumi ya yi barazanar kashe makwabcinsa, ya ɗanɗana kuɗarsa

Rahotanni sun tabbatar da cewa a katafaren gidan Shekarau dake Mundubawa aka yi watandar kudade, sai dai Kaakakin Shekarau, Sule Sule ya bayyana cewa EFCC bata da wata hujja da za ta kai Shekarau kara.

Don kawai na ce Buhari ya gaza shi yasa EFCC ke tuhuma ta da satar kudi – Malam Shekarau

Malam Shekarau
Source: Twitter

Sule yace: “Shekarau ya yi hira a gidan Talabijin na AIT, inda ya bayyana gazawar gwamnatin Buhari, wannan ne ya sanya EFCC dagewa akan lallai sai sun shigar da shi kara a gaban Kotu, duk da cewa basu da wata hujja akansa game da kudi naira miliyan 25 da ake zargin ya amsa cikin kudin kamfe.

“A shekarar 2016 ne EFCC ta fara binciken kudin kamfe din Jonathan da ake zargin an baiwa Malam Shekarau naira miliyan 25, amma ya bayyana musu cewa ko sisi bai karba ba, kuma ya bukaci EFCC su samar da wata hujjar dake nuna ya amshi kudin. Daga bisani suka sallame shi saboda rashin hujja.”

Amma Sule Sule ya bayyana kaduwarsa da a yan kwanakin nan hukumar EFCC ta aiko musu da sakon cewa zata gurfanar da Shekaru a gaban babbar kotun tarayya dake jihar Kano a ranar Alhamis, 24 ga watan Mayu, kuma dai akan wadannan kudade da bai ci ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel