Sanata Shehu Sani yayi martani ga Shugaba Buhari akan harin Birnin Gwari

Sanata Shehu Sani yayi martani ga Shugaba Buhari akan harin Birnin Gwari

Majiyar mu ta samu rahoton cewa, sanatan nan da ba ya barin sai ta kwana mai wakilcin jihar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya kirayi gwamnatin tarayya dangane da inganta tsaro a kasar nan.

Shafin jaridar Daily Post ya ruwaito cewa, Sanatan yayi wannan kira ne musamman dangane da harin da ya afku a Birnin Gwari a karshen makon da ya gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, a ranar Lahadin da ta gabata ne ‘yan ta'adda rike da muggan makamai suka kai hari kan wasu fasinjoji 87 a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna inda suka yi garkuwa dasu.

Sanata Shehu Sani yayi martani ga Shugaba Buhari akan harin Birnin Gwari

Sanata Shehu Sani yayi martani ga Shugaba Buhari akan harin Birnin Gwari

A yayin martani dangane da makamantan wannan hare-hare dake faman afkuwa a kasar nan, sanatan yayi saran sa kan gaba cikin wani sako da ya rubuto a shafin sa na dandalin sada zumunta a ranar Litinin din da ta gabata.

KARANTA KUMA: INEC na shirin amfani da Masu bautar Kasa 15,000 a zaben jihar Ekiti

Sanatan ya rubuta wannan sako kai tsaye zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yake kiran sa cikin gaggawa a kan malalo dukiya da kayan aiki ga hukumomin tsaro na kasar nan da zai tallafa masu wajen kawo karshen ta'addanci.

Ya ci gaba cewa, wannan ita kadai ce hanya da za ta taimaka wajen tabbatar da tsaro da kuma kwanciyar hankullan al'umma musamman na Birnin Gwari dake jihar sa ta Kaduna.

Ya kara da cewa, lokaci yayi da ya kamata a kawo karshen zubar da jini da ta'addanci na garkuwa da mutane a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel