Yanzu Yanzu: Ni bazan amsa maku wata tambaya ba - Omo-Agege ga kwamitin bincike

Yanzu Yanzu: Ni bazan amsa maku wata tambaya ba - Omo-Agege ga kwamitin bincike

- Dan majalisa Ovie Omo-Agege, a ranar Talata, ya fadawa kwamitin bincike cewa shi bazai ce masu komai ba game da lamarin da suka gayyaci akai ba

- Shuwagabannin majalisu ne suka kafa kwamitin domin suyi bincike akan lamarin shiga majalisar da akayi aka saci sandar girma a watan da ya gabata

- Kwamitin sun gayyaci Omo-Agege domin ya basu bayani game da inda yake da hannu a cikin lamarin na jagorantar ‘yan ta’adda zuwa cikin majalisa, inda suka saci sandar girma

Dan majalisa Ovie Omo-Agege, a ranar Talata, ya fadawa kwamitin bincike cewa shi bazai ce masu komai ba game da lamarin da suka gayyaci akai ba.

Shuwagabannin majalisu ne suka kafa kwamitin domin suyi bincike akan lamarin shiga majalisar da akayi aka saci sandar girma a watan da ya gabata.

Kwamitin sun gayyaci Omo-Agege domin ya basu bayani game da inda yake da hannu a cikin lamarin na jagorantar ‘yan ta’adda zuwa cikin majalisa, inda suka saci sandar girma.

Yanzu Yanzu: Ni bazan amsa maku wata tambaya ba - Omo-Agege ga kwamitin bincike

Yanzu Yanzu: Ni bazan amsa maku wata tambaya ba - Omo-Agege ga kwamitin bincike
Source: Depositphotos

Omo-Agege ya bayyanawa kwamitin cewa ya shigar da kara kotu, inda yace fadar wani abu game da aukuwar lamarin ko hannu da yake dashi a cikin lamarin wata rijiyace akeso ayi masa ya fada ciki, don a samu abunda za’ayi amfani dashi a bata masa suna a idon jama’a.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sanatoci na ganawar sirri da Buhari kan lamarin Saraki da IGP

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa Wakilan majalisa zasu gana da shugaba Muhammadu Buhari a yau Talata, a bisa ikirarin da Saraki ya keyi na cewa shugaban ‘Yan Sanda Ibrahim Idris na farautarsa, yana kokarin laka masa sharri ta hanyar alakantashi da wasu ‘yan ta’adda. R

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel