Yanzu-yanzu: An saka labule tsakanin Sanatocin APC da Oshiomhole

Yanzu-yanzu: An saka labule tsakanin Sanatocin APC da Oshiomhole

Ana can ana wata ganawar sirri tsakanin sanatocin najeriya ‘yan jam’iyyar APC da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, a Abuja.

An hana jami’an tsaro shiga wurin taron da aka farad a misalign karfe 3:30 na ranar yau, Talata.

Ziyarar Oshiomhole ga Sanatocin jam’iyyar APc ba zata rasa nasaba da kudirin san a son zama shugaban jam’iyyar na kasa ba.

Oshiomhole ya kai makanciyar irin wannan ziyara ga mambobin majalisar wakilai cikin satin da ya gabata.

Yanzu-yanzu: An saka labule tsakanin Sanatocin APC da Oshiomhole

Adams Oshiomhole

Za gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa ranar 2 ga watan Yuni, 2018 inda ake kyautata zaton Oshimhole zai maye gurbin shugaban jam’iyyar mai baring ado, Cif John Oyegun.

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar, wata kotu a jihar Sokoto ta tisa keyar tsohon mataimakin gwamnan jihar, Mukhtar Shagari, da wasu 'yan PDP hudu ya zuwa gidan yari bayan an gurfanar da su bisa tuhumar su da almundahanar kudi da adadin su ya kai miliyan N500m.

DUBA WANNAN: Matashi ya zubar da hakoran ubangidan sa da guduma a kan albashin wata 5

Ragowar wadanda ake tuhuma tare da tsohon mataimakin gwamnan sune; toshon kwamishinan ilimin jihar, Ibrahim Gidado, Ma’;ajin jam’iyyar PDP, Nasiru Dalhatu, shugaban jam’iyyar PDP, Ibrahim Milgoma dad an takara tan a gwamna a zaben 2015, Abdallah Wali.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta gurfanar das u ne bisa laifukan da suka hada da safarar kudi da kuma almundahana, laifukan da suka saba da sashe na 16(2)(b) na kundin hana safarar kudi na shekarar 2011.

Kudin da suka wawura sun zo ne daga ofishin tsohuwar minister man fetur ta kasa dake fama da tuhume-tuhumen cin hanci, Diezani Allison Madueke.

Alkalin kotun, Saleh Idrissa, ya daga sauraran karar ya zuwa ranar 24 ga watan Mayu, 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel