Mun shirya tsaf don farfado da Jirgin saman Najeriya nan da ‘yan watanni – Gwamnatin tarayya

Mun shirya tsaf don farfado da Jirgin saman Najeriya nan da ‘yan watanni – Gwamnatin tarayya

- Abin ya kusa faruwa ga 'yan Najeriya, sauran kiris Jirgin sama mallakar kasar ya dawo aiki

- Wani babban Darakta ne ya jaddada hakan yau a Abuja

- Sai dai a wannan karon Jirgin ko ya dawo aiki ba zai zamo mallakar Gwamnati zalla ba

A yau Talata Gwamnatin tarayya ta sake jaddada aniyarta ta farfado da sabon jirgin saman Najeriya a watan Disambar wanann shekarar da muke ciki 2018.

Mun shirya chaf don farfado da Jirgin saman Najeriya nan da ‘yan watanni – Gwamnatin tarayya

Mun shirya chaf don farfado da Jirgin saman Najeriya nan da ‘yan watanni – Gwamnatin tarayya

Daraktan hukumar dake lura da samar da ababen more rayuwa ta kasa, (ICRC) Mr Chidi Izuwah ne ya bayar da tabbacin yayin wata hira da manema labarai a Abuja

Yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa kwamitin farfado da Jirgin sama na kasa umarnin yin aiki tukuru a ragowar wa’adin watanni shida da suka rage domin ganin an samu nasara.

KU KARANTA: Ba bu lallai Najeriya na da halin biyan Basussukan ta - IMF

Chidi Izuwah wanda mamba ne a kwamitin kokarin farfado da kamfanin jirgin saman na kasa ya ce, yunkurin zai kasance hadin gwuiwa ne da barin gwamnati da kuma masu zaman kansu domin dorewar tsarin.

“Kwamitin kowanne bari sun gamu kuma an tattauna yadda za’a bullo da daftarin kasuwanci, wanda sai da shi ne Kamfanoni masu zaman kansu suke amincewa suyi hulda don cin riba.”

A cewarsa, farfado Jirgin saman kasa abu ne mai mutukar kyau da zai taima wajeen farfado da tattalin arzikin kasar nan da kuma samar da aiyukan yi kamar yadda hakan ke faruwa a sauran kasashen duniya.

Sannan ya kara da cewa mallakar Jirgin sama na kasa wani abu ne da kowa zai yi alfahari da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel