Kada ku jawo rikicin addini - Sultan ya roki shugabannin addinin kirista

Kada ku jawo rikicin addini - Sultan ya roki shugabannin addinin kirista

- Sultan Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, yayi kira ga shuwagabannin addinin kirista na kasa da su kiyayi fadin maganganu babu hangen nesa a ciki saboda hakan zai sa ‘yan ta’adda suyi nasara akan yakin da suke yi da Najeriya

- Jagoran wanda yayi bayanin a madadin musulmin Najeriya, inda yake gargadin maluman kiristoci game da furunci da suka yi na cewa idan har Leah Sharibu ta mutu a hannun Boko Haram za’ayi yakin addini a kasar

- Sultan ya bayyana irin wadannan kalaman a matsayin kalaman rashin adalci, inda ya kara da cewa ta’addanci ba shi da wani addini ko kabila

Sultan Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, yayi kira ga shuwagabannin addinin kirista na kasa da su kiyayi fadin maganganu babu hangen nesa a ciki saboda hakan zai sa ‘yan ta’adda suyi nasara akan yakin da suke yi da Najeriya.

Jagoran wanda yayi bayanin a madadin musulmin Najeriya, inda yake gargadin maluman kiristoci game da furunci da su kayi na cewa idan har Leah Sharibu ta mutu a hannun Boko Haram za’ayi yakin addini a kasar.

Kada ku jawo rikicin addini - Sultan ya roki shugabannin addinin kirista

Kada ku jawo rikicin addini - Sultan ya roki shugabannin addinin kirista

Sultan ya bayyana irin wadannan kalaman a matsayin kalaman rashin adalci, inda ya kara da cewa ta’addanci ba shi da wani addini ko kabila.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sanatoci na ganawar sirri da Buhari kan lamarin Saraki da IGP

Sultan yace yana mamakin yanda za’ace wai musulmi ya hada kai da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram wurin kama ‘yan mata ‘yan makaranta.

Yace musulmin da kungiyar Boko Haram suka kashe sunfi yawan kiristocin da kungiyar suka kashe.

A halin da ake ciki, Kiristoci sunyi zanga-zangan lumana a jihohin kasar domin nuna rashin jin dadi kan lamarin tsaro a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel