Da duminsa: An tsige mataimakin kakakin majalisar jihar Ondo

Da duminsa: An tsige mataimakin kakakin majalisar jihar Ondo

An tsige mataimakin kakakin majalisar jihar Ondo, Mr. iroju Ogundeji mai wakiltan yankin Odigbo II. 'Yan majalisar sun cinma matsayar tsige shi ne a zaman da majalisar tayi a yau Talata.

An tsige Ogundeji dan jam'iyyar APC ne bayan mambobi 18 cikin 26 da ke majalisar sun sanya hannu a takardan tsigewar kuma aka mika ta ga kakakin majalisar Mr. Bamidele Oloyeloogun.

Yan majalisan basu bayyana dalilan da yasa suka tsige shi ba a yanzu sai dai wata majiya ta shaidawa jaridar Punch cewa an tsige shi ne saboda wasu tuhume-tuhume na saba ka'idojin aiki da aka gabatar a kansa.

Da duminsa: An tsige mataimakin kakakin majalisar jihar Ondo

Da duminsa: An tsige mataimakin kakakin majalisar jihar Ondo

Wata majiyar daban kuma ta ce an tsige shi ne saboda wata rashin jituwa da ta faru tsakaninsa da kakakin majalisar.

Tsohon mataimakin kakakin majalisar yana daya daga cikin yan majalisa 18 da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC bayan gwamna Rotimi Akeredolu ya yi nasarar lashe zaben zama gwamna a 2017.

A halin yanzu, an maye gurbin Ogundeji da Mr. Bimbo Fajolu wanda ke wakiltan mazabar Ile Oluji/Oke Igbo a jihar ta Ondo.

An raka tsohon mataimakin kakakin majalisar waje yayin da majalisar ta cigaba da zamanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel