Yan Sanda sun kama mambobin kungiyar MASSOB 50 a garin Aba

Yan Sanda sun kama mambobin kungiyar MASSOB 50 a garin Aba

- Sama da mambobin kungiyar MASSOB 50 ne suka shiga hannun jam’ian tsaro na hukumar ‘Yan Sanda a garin Aba

- MASSOB sun bayyana ranar 22 ga watan Mayu, a matsayin ranar bikin neman ‘yancin kabilar Igbo Najeriya na Biafra, wanda Cif Ralph Uwazuruike ya jagoranta

- Labari ya bayyana cewa ‘yan Sanda sun kama ‘yan kungiyar MASSOB a Osisioma Ngwa, akan hanyar Enugu-Port Harcourt, bayan jami’an ‘Yan Sanda su sama da 15 sun harba masu barkonon tsohuwa

Sama da mambobin kungiyar MASSOB 50 ne suka shiga hannun jam’ian tsaro na hukumar ‘Yan Sanda a garin Aba.

MASSOB sun bayyana ranar 22 ga watan Mayu, a matsayin ranar bikin neman ‘yancin yan kabilar Igbo a Najeriya na Biafra, wanda Cif Ralph Uwazuruike ya jagoranta, a 175 Fault road, Aba a ranar 22 ga watan Mayu, 2000.

Yan Sanda sun kama mambobin kungiyar MASSOB 50 a garin Aba

Yan Sanda sun kama mambobin kungiyar MASSOB 50 a garin Aba

Labari ya bayyana cewa ‘yan Sanda sun kama ‘yan kungiyar MASSOB a Osisioma Ngwa, akan hanyar Enugu-Port Harcourt, bayan jami’an ‘Yan Sanda su sama da 15 sun harba masu barkonon tsohuwa.

KU KARANTA KUMA: Mahaifin budurwar da saurayinta ya kashe ya fadawa saurin nata cewa sai ya auri gawar diyar tasa

Shugaban kungiyar MASSOB na Abia ta yankin kudu, Fred Onyenaucheya, ya nuna rashin jin dadinsa akan kam ‘yan kungiyar dake neman ‘yancin Biafra da akayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel