Yanzu Yanzu: Sanatoci na ganawar sirri da Buhari kan lamarin Saraki da IGP

Yanzu Yanzu: Sanatoci na ganawar sirri da Buhari kan lamarin Saraki da IGP

A yanzu haka Sanatocin da aka wakilta na cikin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa dake Villa, Abuja.

Abokan aikinsu ne suka nada yan majalisar karkashin jagorancin shugaban maalisar dattawa Bukola Saraki domin su tattauna da shugaban kasa Buhari kan lamarin rikici dake gudana da babban sufeto janar nayan sanda, Ibrahim Idris.

Shugaban majalisa Bukola Saraki a ranar Laraba yayi ikirarin cewa Idris na shirya wasu hanyoyi na kulla masa sharri a wurin shari’ar wasu ‘yan ta’adda wadanda aka kama a jihar Kwara.

A ranar Laraba ‘yan majalisar suka yanke shawarar zuwa su sanar da shugaban kasa halin da shugaban ‘Yan Sandan ke ciki, bayan zargin da Saraki yake masa na kokarin kulla masa sharri.

Yanzu Yanzu: Sanatoci na ganawar sirri da Buhari kan lamarin Saraki da IGP

Yanzu Yanzu: Sanatoci na ganawar sirri da Buhari kan lamarin Saraki da IGP

Saraki ya bayyanawa ‘yan majalisar cewa Gwamna Abdulfatah Ahmed ne ya fada masa cewa an mayar da wadanda ake zargin zuwa birnin tarayya domin hukuntasu kamar yadda shugaban ‘Yan Sandan ya bayar da umurni.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Metuh ya yanke jiki ya fadi ne da gangan - Alkali

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa Wakilan majalisa zasu gana da shugaba Muhammadu Buhari a yau Talata, a bisa ikirarin da Saraki ya keyi na cewa shugaban ‘Yan Sanda Ibrahim Idris na farautarsa, yana kokarin laka masa sharri ta hanyar alakantashi da wasu ‘yan ta’adda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel