Kaji irinta: Kotu ta yankewa wasu Mutane 3 hukuncin wata 5 a gidan kurkuku bayan sun saci Lasifika da Makirfon Coci

Kaji irinta: Kotu ta yankewa wasu Mutane 3 hukuncin wata 5 a gidan kurkuku bayan sun saci Lasifika da Makirfon Coci

- Kowa ya ja ruwa, shi ruwa kan daka, wasu Mutane sun gurfana gaban kotu

- Mai shari'ar ya kuma yanke musu hukunci dai-dai da abinda suka aikata

- watakila idan har ba su cika sharuddan da ya gindaya musu ba zasu karasa Azuminsu a garkame

Wata Kotu dake zamanta a Kubwa ta birnin tarayya Abuja ta ingiza keyar wasu Mutane 3 gidan yari, sakamakon kama su da laifin satar bututun magana da kuma Lasifikar Coci.

Kaji irinta: Kotu ta yankewa wasu Mutane 3 hukuncin wata 5 a gidan kurkuku bayan sun saci Lasikika da Makirfon Coci

Kaji irinta: Kotu ta yankewa wasu Mutane 3 hukuncin wata 5 a gidan kurkuku bayan sun saci Lasikika da Makirfon Coci

‘Dan sanda mai gabatar da kara Babajide Olanipekun ya shaidawa kotun cewa, Cocin Redeemed Christian ce ta shigar da karar ofishinsu a ranar 13 ga watan Mayu.inda suka yi korafin an fasa musu taga an saci Fankoki da kudin kowacce ya kai N7, 500 da kuma bututun amsa kuwwa da kudinsu zai kai N50, 000 da Lasifika ta N70, 000 da Makirfo da yakai N24,000 da kuma jitar kida da kudinta ya kai N50, 000.

Amma ‘Yan sanda sun samu nasarar karbo kayan sai dai kawai na’urar Amsa kuwwa da Makirfo da na’urar sauti ne ba’a samu ba.

KU KARANTA: Da duminsa: ‘Yan Bindiga sun yi garkuwa da Matar Kwamishina da ‘ya’yansa 6 a Zamfara

An bayyana sunayen wadanda ake zargin da Mustapha Haruna, Biliya Usman, da kuma Ibrahim Sani.

Da yake yanke musu hukuncin a yau Talata, al’akalin kotun mai shari’a Mohammed Marafa ya tabbatar da kama su dumu-dumu da laifin hada kai da haurawa tare da dauke kayan.

Amma ya basu damar zabar biyan tarar Naira N15, 000 kowannensu. Sannan ya yankewa wani mai suna Ibrahim Abubakar hukuncin wata 6 ko biyan tarar Naira 20,000 da kuma Bulala 3 bisa karbar kayan sata, inda ya ce ba don barawan zaune ba da tabbas ba’a samu na tsaye ba.

Daganan ne mai shari’ar ya shawarci masu kara da su shigar da karar neman a biya su kayan da ba'a kaiga gano su ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel