Satan sandar majalisa: Sanata Omo-Agege da Ali Ndume ya bayyana gaban kwamitin bincike

Satan sandar majalisa: Sanata Omo-Agege da Ali Ndume ya bayyana gaban kwamitin bincike

Sanata mai wakilta Delta ta tsakiya, Ovie Omo-Agege da Sanata mai wakiltan Borno ta kudu, Sanata Ali Ndume, a yanzu haka suna bayyana gaban kwamitin majalisan dokokin tarayya da aka nada domin gudanar da bincike kan abubuwan da suka tattari satan sandar majalisa ranan 18 ga watan Afrilu, 2018.

Kafin yau, sanata Omo Agege ya kai majalisan kotu domin dakatad da wannan bincike. Zaku tuna cewa a amkon da ya gabata kwamitin ta aika sakon gayyata ga sanata Omo-agege da Sanata Ali Ndume kan zargin da ake musu na hannu cikin satan sandar.

Shugaban kwamitin, Sanata Bala Ibn Na’Allah, ya bayyana cewa jawaban jami'an tsaro ga kwamitin ya nuna cewa Sanatocin guda biyu na da hannu cikin abinda ya faru.

Satan sandar majalisa: Sanata Omo-Agege ya bayyana gaban kwamitin bincike

Satan sandar majalisa: Sanata Omo-Agege ya bayyana gaban kwamitin bincike
Source: Depositphotos

Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa ba shi da hannu cikin wannan abu amma duk da haka, zai iya bayyana gaban kwamitin binciken.

KU KARANTA: Watanmu 44 ba a biya mu albashi ba – Ma’aikata

A karshen makon da ya gabata, sanata Ali Ndume ya caccaki shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, kan yadda yake gudanar da shugabancin majalisar. Ya bayyana nadamarsa na bada gudunmuwa wajen zaben Saraki a matsayin shugaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel