Da duminsa: ‘Yan Bindiga sun yi garkuwa da Matar Kwamishina da ‘ya’yansa 6 a Zamfara

Da duminsa: ‘Yan Bindiga sun yi garkuwa da Matar Kwamishina da ‘ya’yansa 6 a Zamfara

- Matsalar tsaro na dada kamari a jihar Zamfara,

- A jiya da daddare wasu 'yan Bindiga sun kai hari gidan wani dan siyasa

- Amma har ya zuwa yanzu ba su nemi kudin fansa ba

Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa, ‘yan Bingida sun yi garkuwa da Matar wani Kwamishina da ‘ya’yansa 6 a Talata a kauyen Gurbin Bore dake jihar Zamfara.

Da duminsa: ‘Yan Bindiga sun yi garkuwa da Matar Kwamishina da ‘ya’yansa 6 a Zamfara

Da duminsa: ‘Yan Bindiga sun yi garkuwa da Matar Kwamishina da ‘ya’yansa 6 a Zamfara

An dai rawaito cewa ‘yan garkuwar sun kai hari gidan Kwamishinan Matasa da wasanni da koyar da sana’o’i Alhaji Abdullahi Gurbin a karamar hukumar Zurmi da misalign karfe 1:30am na dare.

KU KARANTA: Karya ne, Magu baya neman zama Gwamnan Borno - EFCC

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamishinan ya fadawa manema labarai a garin Gusau, ya ce sun tafi da Matarsa da kuma ‘ya’yana 3 tare da karin wasu ‘ya’yan riko 3 da suke gidansa.

“Amma har ya zuwa yanzu ba su nemi fansa daga gare mu ba, amma daim un kai rahoton faruwar iftila’in ofishin ‘yan sanda.” Alhaji Abdullahi ya fada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel