Sanata Ndume: Nayi nadamar goyawa Saraki baya

Sanata Ndume: Nayi nadamar goyawa Saraki baya

- Sanata Ali Ndume (APC - Borno ta kudu), yace yayi nadamar goyawa shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki baya wurin samun damar hayewa kujerar shi

- Ndume, wanda ya zargi Saraki da laifin zubarwa majalisar mutunci, yayi magana a wani shiri na gidan talabijin Channels a ranar juma'ar nan da dare

Sanata Ndume: Nayi nadamar goyawa Saraki baya

Sanata Ndume: Nayi nadamar goyawa Saraki baya

Sanata Ali Ndume (APC - Borno ta kudu), yace yayi nadamar goyawa shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki baya wurin samun damar hayewa kujerar shi. Ndume, wanda ya zargi Saraki da laifin zubarwa majalisar mutunci, yayi magana a wani shiri na gidan talabijin Channels a ranar juma'ar nan da dare.

An tambayeshi ko yayi dana sanin goyon bayan Saraki da yayi ya samu shugabancin majalisar, ya amsa da: "Eh, nayi"

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa Allah ya bawa shugaba Buhari nasara a zaben 2015 - Sanata Gyunka

"Duba majalisar yanzu, an rage mata nagarta, saboda wasu mutane kadan daga cikin mu da sukayi kuskure. Bana son in fito in fada sunayen su. Ina fadin gaskiya, kuma koda zan rage ni kadai ne, zan tsaya akan gaskiya ta. "

"Mun fara zancen wanda zai rike kujerar shugabancin hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu. Nayi magana akan hakan a gidan talabijin yanzu maganar ta zama tarihi. Sai muka kuma yi magana akan motocin da za'a shigo dasu da kuma zancen shaidar kammala makarantar Dino Melaye. Wanda abin mamaki kawai aka dakatar dani na kwanaki 180 kuma ba kwamitin bane suka bukaci hakan."

"Abokan aikina basu san dalilin da yasa aka dakatar dani ba bisa ka'ida ba kuma babu bin tsarin kundin tsarin mulki har na kwanaki 180."

"Saboda haka ne, hankali kwance na kai kara kotu. Bai dace ba ace wanda yasan 'yancin shi, ya dinga daga kanshi. Yana amfani da karfin kujerar shi ba bisa doka ba. Kamar yanda kundin tsarin mulki yace ' Shugaban majalisa, shugabanci kadai zaiyi, ko kuri'a bashi da ita ballantana zabi.'

A lokacin da ka amince da shugabantar majalisar, toh fa ka rasa wasu hakkokinka na majalisar har sai in majalisar ce ta baka, wannan kuwa zai faru ne in aka sauke ka. "

" Shugaban majalisar bai da ikon bada umarni sai wanda majalisa ta amince dashi, daga haka ne ake farawa saboda kawai mutum yana tunanin kowa yana karkashin sa sai ya dinga yin abin da ya ga dama."

" Tunanin mutane 108, yafi na mutum daya, amma yanzu dai majalisar ta zama kamar ta Dino da Saraki ce. Gaskiya wannan abun takaici ne. "

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel