Dalilin da yasa Allah ya bawa shugaba Buhari nasara a zaben 2015 - Sanata Gyunka

Dalilin da yasa Allah ya bawa shugaba Buhari nasara a zaben 2015 - Sanata Gyunka

Sanata mai wakiltar jihar Nasarawa ta arewa, Sanata Philip Gyunka, ya Allah ya bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari nasarar lashe zaben shugaban kasa ne a shekarar 2015, saboda yana so ya shaidawa duniya cewa babu abinda Buharin zai iya a Najeriya

Dalilin da yasa Allah ya bawa shugaba Buhari nasara a zaben 2015 - Sanata Gyunka

Dalilin da yasa Allah ya bawa shugaba Buhari nasara a zaben 2015 - Sanata Gyunka

Sanata mai wakiltar jihar Nasarawa ta arewa, Sanata Philip Gyunka, ya Allah ya bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari nasarar lashe zaben shugaban kasa ne a shekarar 2015, saboda yana so ya shaidawa duniya cewa babu abinda Buharin zai iya a Najeriya. Sannan kuma ya nuna farin cikin sa game da irin rikicin da jam'iyyar APC mai mulki ke ciki, inda ya bayyana hakan a matsayin gagarumar nasara ga jam'iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Jerin kasashen da suke awanni 22 suna azumi

Da yake magana a karamar hukumar Arochukwu dake jihar Abia, a lokacin da jam'iyyar ta PDP take kaddamar da wani taro, Sanata Gyunka, wanda ya raka Sanata Mao Ohuabunwa zuwa wurin taron, yace jam'iyyar PDP jam'iyya ce da a yanzu duniya take kallo domin ta kawo canjin da jam'iyyar APC ta kasa kawowa al'umma.

Sanatan yace, "Idan nace canji ina nufin canji mai amfani, ba irin canjin da muke ciki ba a yanzu na bala'i da wahalar rayuwa, jam'iyyar APC mai mulki ta jefa cikin tashin hankalin da a tarihin kasar nan ba a taba shiga ba.

"Abinda yake faruwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari dama ce babba ga jam'iyyar mu ta PDP. Inda ace shugaba Buhari bai ci zabe ba da tuni yanzu ana ta cigaba da zagin mu. Allah ya kawo shine saboda ya tona asirin sa, akan bashi da wani abu da zai iya yiwa Najeriya," inji shi.

A lokacin da yake bayani ga al'ummar karamar hukumar Arochukwu, shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Cif Johnson Onuigbo, yace Najeriya tayi asarar duk abubuwan da ta samu kafin zuwan jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel