Hadimin Shugaba Buhari ya mayar da martani ga Hadimin Jonathan

Hadimin Shugaba Buhari ya mayar da martani ga Hadimin Jonathan

Mallam Garba Shehu, babban hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan hulda da manema labarai, ya nemi

Da sanadin shafin jaridar Daily Post, mun samu rahoton cewa mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu, ya yi caccaka ta martani ga Reno Omokri, kakakin na musamman ga tsohon shugaban kasa Gooluck Jonathan.

Jaridar dai ta ruwaito cewa, Mallam Garba kai tsaye ya tuhumi hadimin na tsohuwar gwamnati akan su dawo wa da 'yan Najeriya kudaden da suka wawushe yayin da suke cin karen su babu babbaka.

Hadimin Shugaba Buhari ya mayar da martani ga Hadimin Jonathan

Hadimin Shugaba Buhari ya mayar da martani ga Hadimin Jonathan

Mallam Garba dai ya shaidawa Omokri cewa, da shi da makarraban sa su manta da sake gudanar da wasu al'amurra a cikin kasar nan ta Najeriya, inda yace idan har su na mafarki akan hakan to kuwa su tashi su farga.

KARANTA KUMA: Uche Secondus da Wasu Jiga-Jigan Jam'iyya na fuskantar Barazana ta APC - PDP

Legit.ng ta fahimci cewa, Mallam Garba yayi wannan caccaka ne a shafin sa na sada zumunta, inda kai tsaye ya shadaiwa Omokri cewa su dawo wa da 'yan najeriya kudaden su da aka wawushe karkashin gwamnatin ubangidan sa watau Jonathan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel