A kawo mana dauki: Watanmu 44 ba a biya mu albashi ba – Ma’aikata

A kawo mana dauki: Watanmu 44 ba a biya mu albashi ba – Ma’aikata

- Ma'aikatan Noma na cikin mawuyacin hali a jihar Adamawa

- Sunyi zan-zangar lumana bayan shafe shekaru ba tare da an biya su albashi ba

- Bayan gudanar da zanga-zangar ne suka kai kukansu ga Gwamnan jihar

Ma’aikatan Kamfanin Noma mallakar gwamnatin jihar Adamawa mai suna Adamawa Agricultural Development and Investment Ltd (AADIL), sun bukaci gwamnan jihar Muhammadu Bindow ya kai musu dauki sakamakon rashin biyansu albashinsu har na tsawon watanni 44.

A kawo mana dauki: Watanmu 44 ba a biya mu albashi ba – Ma’aikata

A kawo mana dauki: Watanmu 44 ba a biya mu albashi ba – Ma’aikata

Ma’aikatan sun bayyana hakan ne a yayin da suke mika wasikar dake dauke da korafinsu ga ofishin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) bayan sun gudanar da zanga-zangar lumana a jiya Litinin a garin Yola. A cewarsu rabon da a biya su albashinsu tun shekarar 2014.

An dai kafa Kamfanin ne tun a shekarar 2010 domin taimakawa Manoman karkara a jihar, kuma ya koyar da a kalla Manoma 85,000 dabarun Noman zamani kafin Kamfanin ya samu tsaiko a dakatar da aiyukansa.

KU KARANTA: Ba za mu daina magana a kan APC ba – Sanata Shehu Sani

A cikin wasikar sun bayyana cewa bisa yadda Gwamnan jihar yake baiwa bangaren Noma muhimmanci ne kamar yadda kudurin shugaba Muhammadu Buhari ya na farfado da harkar Noma ne suka ga dawo da Kamfanin nan AADIL zai mutukar taimakwa dazar an maido shi aiki yadda ya kamata.

A kawo mana dauki: Watanmu 44 ba a biya mu albashi ba – Ma’aikata

A kawo mana dauki: Watanmu 44 ba a biya mu albashi ba – Ma’aikata

Domin a lokacin da Kamfanin yake aiki sosai ya taimaka wajen samar da irin shuka da na dabbobi da harkar noman Kifi da na Kaji da sauransu.

A don haka ne suka bukaci Gwamnatin jihar da ta gaggauta daukar matakin da ya dace domin Kamfanin na AADIL baya samun kulawar da ta kamata.

Sai dai duk wani kokari da majiyarmu tayi don magana da shugaban Kamfanin Usman Aji, ya ci tura domin sai an na sama da shi sun amince yayi magana tukunna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel