Sanatan Kaduna Shehu Sani ya nemi a ba Jami’an tsaro makamai a Birnin Gwari

Sanatan Kaduna Shehu Sani ya nemi a ba Jami’an tsaro makamai a Birnin Gwari

- Sanata Shehu Sani na Kaduna ta Tsakiya ya koka da halin Birnin-Gwari

- ‘Dan Majalisar na Jihar Kaduna yace sai Gwamnatin Buhari tayi da gaske

- Shehu Sani ya nemi a karawa Jami’an tsaro kayan aiki domin kare jama’a

Mun samu labari cewa Sanatan Kaduna ta tsakiya da ke karkashin Jam’iyyar APC mai mulkin kasar watau Shehu Sani yayi kira ga Shugaban kasa Buhari ya kara karfin Jami’an tsaro a cikin Jihar Kaduna.

Sanatan Kaduna Shehu Sani ya nemi a ba Jami’an tsaro makamai a Birnin Gwari

Shehu Sani yace ‘Yan ta’adda sun fi karfin Sojoji a Birnin Gwari

Sanatan na Kaduna ta tsakiya yace a halin yanzu an fi karfin Sojojin Najeriya da ke Garin Birnin Gwari. ‘Dan Majalisar yace idan har ana so ayi maganin wannan rikici a kare jama’a tun da wuri dole Gwamnatin Tarayya ta tashi tsaye.

‘Dan Majalisar Dattawan yace ayi maza-maza a ba ‘Yan Sanda da Sojojin Kasar da ma sauran Jami’an tsaro na DSS da NSCDC manyan makamai domin su yi galaba kan Tsagerun da ke barna a Yankin na Dajin Birnin Gwari na tsawon lokaci.

KU KARANTA: Babu abin da zai sa mu daina fadawa Jam’iyyar APC gaskiya Inji Sani

Duk da cewa Gwamnati ta kara Jami’an tsaro a Yankin har yanzu ana kashe jama’a. Sani yace ana kashe ‘Yan Gari da ma Jami’an tsaro, bayan nan kuma ana yi wa mata fyafe, a saci dabbobi, a tsere da wasu Bayin Allah har da yi wa jama’a fashi.

Sanatan dai ya saba kokawa da abin da ke faruwa a Yankin da yake wakilta. Har dai ta kai ana tsare masu wucewa ta hanyar ana garkuwa da su. Manoman Garin dai tuni su ka tsere saboda rashin tsaro da yayi yawa a Garin na Birnin Gwari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel