Ba za mu daina magana a kan APC ba – Sanata Shehu Sani

Ba za mu daina magana a kan APC ba – Sanata Shehu Sani

- Sanatan Kaduna na Yankin Tsakiya yace ba zai daina magana game da APC ba

-Ana kuka da yadda ‘Dan Majalisar ke tonawa Jam’iyyar sa asiri a gaban jama’a

- Sanatan na Jihar Kaduna dai ya saba fitowa fili ya ci zarafin Jam’iyyar mai mulki

Jiya ne mu ka ji cewa Sanatan Kaduna ta tsakiya watau Kwamared Shehu Sani yayi bayani a shafin sa na sadarwa na Tuwita inda yace don su na ‘Ya ‘yan APC ba za su daina magana kan Jam’iyyar ba.

Ba za mu daina magana a kan APC ba – Sanata Shehu Sani
Sanata Shehu Sani yace zai cigaba da fadawa APC gaskiya

‘Dan Majalisar Dattawan dai yace don su na ‘Yan Jam’iyya ace ba za su yi magana kan Jam’iyyar a gaban Duniya ba kamar kace ba a za ayi magana a bainar Duniya game da Najeriya bane don kawai mu din ‘Yan Kasa ne.

KU KARANTA: Sanatan APC Dino Melaye ya caccaki Jam'iyyar sa

Ana dai sukar yadda Sanatan yake fitowa a gaban kowa yana bayyana abin da ke damun Jam’iyyar da kuma cusa baki cikin rikicin cikin-gidan Jam’iyyar a shafin sadarwa maimakon ya samu manyan Jam’iyyar su zauna.

Sanatan dai cikin gatse ya koka da yadda Jam’iyyar APC ta gaza cika alkawarin da tayi wa ‘Yan Najeriya na kawo canji a Kasar a 2015. ‘Dan Majalisar ya kuma yi kira ga Shugaban Kasa ya karawa Jami’an tsaro karfi a Birnin Gwari.

Dazu kun ji cewa Sanata Ali Ndume da ake hira da shi a Talabijin yace Bukola Saraki ya maida Majalisar Dattawa tamkar gidan sa inda ya ma nuna cewa idan ta kama zai fede biri har wutsuya a gaban Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel