Wakilan majalisa zasu gana da shugaba Buhari a yau game da lamarin dake tsakanin Saraki da IGP

Wakilan majalisa zasu gana da shugaba Buhari a yau game da lamarin dake tsakanin Saraki da IGP

- Wakilan majalisa zasu gana da shugaba Muhammadu Buhari a yau Talata, a bisa ikirarin da Saraki ya keyi na cewa shugaban ‘Yan Sanda Ibrahim Idris na farautarsa

- Shugaban majalisa Bukola Saraki a ranar Laraba yayi ikirarin cewa Idris na shirya wasu hanyoyi na kulla masa sharri a wurin shari’ar wasu ‘yan ta’adda wadanda aka kama a jihar Kwara

- Saraki ya bayyanawa ‘yan majalisar cewa Gwamna Abdulfatah Ahmed ne ya fada masa cewa an mayar da wadanda ake zargin zuwa birnin tarayya domin hukuntasu kamar yadda shugaban ‘Yan Sandan ya bayar da umurni

Wakilan majalisa zasu gana da shugaba Muhammadu Buhari a yau Talata, a bisa ikirarin da Saraki ya keyi na cewa shugaban ‘Yan Sanda Ibrahim Idris na farautarsa, yana kokarin laka masa sharri ta hanyar alakantashi da wasu ‘yan ta’adda.

Shugaban majalisa Bukola Saraki a ranar Laraba yayi ikirarin cewa Idris na shirya wasu hanyoyi na kulla masa sharri a wurin shari’ar wasu ‘yan ta’adda wadanda aka kama a jihar Kwara.

A ranar Laraba ‘yan majalisar suka yanke shawarar zuwa su sanar da shugaban kasa halin da shugaban ‘Yan Sandan ke ciki, bayan zargin da Saraki yake masa na kokarin kulla masa sharri.

Wakilan majalisa zasu gana da shugaba Buhari a yau game da lamarin dake tsakanin Saraki da IGP

Wakilan majalisa zasu gana da shugaba Buhari a yau game da lamarin dake tsakanin Saraki da IGP

Saraki ya bayyanawa ‘yan majalisar cewa Gwamna Abdulfatah Ahmed ne ya fada masa cewa an mayar da wadanda ake zargin zuwa birnin tarayya domin hukuntasu kamar yadda shugaban ‘Yan Sandan ya bayar da umurni.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: EFCC ta shirya gurfanar da Shagari da sauran jiga-jigan PDP a Sokoto

A halin da ake ciki, Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta shirya gurfanar da wani tsohon ministan albarkatun ruwa kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto Alhaji Murkhtar Shagari a gaban wata babban kotun tarayya dake Sokoto a ranar Talata.

Wanda za’a gurfanar tare da Shagari akwai dan takarar gwamna na PDP a zaben 2015, Sanata Abdullahi Wali, ciyaman na PDP na jihar, Alhaji Ibrahim Milgoma, wani tsohon kwamishina, Alhaji Ibrahim Gidado da kuma Alhaji Nasiru Bafarawa, kanin tsohon gwamnan jihar Attahiru Bafarawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel