INEC na shirin amfani da Masu bautar Kasa 15,000 a zaben jihar Ekiti

INEC na shirin amfani da Masu bautar Kasa 15,000 a zaben jihar Ekiti

Kimanin masu yiwa kasa hidima 15, 000 ne za su yi aikin zaben gwamna na jihar Ekiti da za a gudanar a ranar 14 ga watan Yuli karkashin jagorancin hukumar zabe ta kasa watau INEC.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa babban kwamishinan hukumar, Prince Adedeji Soyebi, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai cikin wani shiri mai taken Daybreak Nigeria aka watsa a gidan talabijin na jihar Ekiti.

INEC na shirin amfani da Masu bautar Kasa 15,000 a zaben jihar Ekiti

INEC na shirin amfani da Masu bautar Kasa 15,000 a zaben jihar Ekiti

Soyebi ya bayyana cewa, wannan shiri da hukumar ta kudirta wajen amfani da masu yiwa kasa hidima yayin gudanar da zaben tana daya daga cikin manufofi ta tabbatar da zabe na gaskiya da aminci.

KARANTA KUMA: Ababe 4 da ya kamata ku sani game da Sabuwar Amaryar Masarautar Ingila

Ya kuma bayar da tabbacin cewa hukumar ta hada gwiwa da hukumomin tsaro domin kare lafiyar ma'aikata da ababen gudanar da zabe.

Shugaban hukumar ya kuma bayar da tabbaci da jam'iyyu da masu kada kuri'u akan gudanar da zaben na hakikanin gaskiya mai tattare da adalci gami da aminci.

Legit.ng ta fahimci cewa, Soyebi ya kirayi jam'iyyu akan gabatar da sunayen wakilansu ga hukumar bisa ga tsari na dokokin da aka gindaya a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel