Shekarau da Wali zasu bayyana Ofishin EFCC a yau, akan maganar kudin kamfen N950m

Shekarau da Wali zasu bayyana Ofishin EFCC a yau, akan maganar kudin kamfen N950m

- Ana bukatar ganin tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau tare da Ambassador Aminu Wali da Engr. Mansur Ahmed a ofishin EFCC reshen jihar Kano a yau

- Ibrahim Shekarau da Aminu Wali da kuma Mansur Ahmed zasu bayyana a ofishin na EFCC ne akan kudaden da ake zargin sun kasa N950m a gidan Ibrahim Shekarau gabanin zuwan zaben shekarar 2015

- Ghali Sadiq, mai magana da yawun tsohon gwamnan Ibrahim Shekarau yace Uban gidan nasa bai karbi komai ba a cikin kudaden

Daily Trust ta ruwaito cewa, ana bukatar ganin tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau tare da Ambassador Aminu Wali da Engr. Mansur Ahmed a ofishin hukumar yaki da rashawa ta EFCC reshen jihar Kano a yau da misalin karfe 2 na rana.

Ibrahim Shekarau da Aminu Wali da kuma Mansur Ahmed zasu bayyana a ofishin na EFCC ne akan kudaden da ake zargin sun kasa N950m, a gidan Ibrahim Shekarau gabanin zuwan zaben shekarar 2015 a tsakanin ‘yan jam’iyyarsu ta PDP.

Injiniya Ahmed Mansur, tsohon kwamishinan ayyuka ne a jihar Kano kuma mataimakin Daraktan kamfen na arewacin Najeriya, na tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.

Shekarau da Wali zasu bayyana Ofishin EFCC yau, akan maganar kudin kamfen N950m

Shekarau da Wali zasu bayyana Ofishin EFCC yau, akan maganar kudin kamfen N950m

Daily Trust ta bayar da rahoton cewa Shekarau ta hanyar Ghali Sadiq, mai magana da yawunsa yace Uban gidan nasa bai karbi komai ba a cikin kudaden N950m, wadanda aka kasa a cikin gidan nasa.

KU KARANTA KUMA: 2019: Ka shirya shan kashi – PDP ga Buhari

Sadiq ya bayyana cewa Ambassador Wali ya kakkasa kudaden a tsakanin mambobin jam’iyyar PDP a gidan Ibrahim Shekarau dake jihar Kano.

A halin da ake ciki, mun samu labari cewa Sanatan Borno ta Kudu Ali Ndume ya je gidan Talabijin na Channels TV yayi kaca-kaca da Majalisar Dattawa karkashin Bukola Saraki da wasu ‘Yan tsirarrun Sanatocin Kasar

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel