Yanzu-Yanzu: Bayan ya zame hanunsa daga sharia'r a jiya, lauyan Olisa Metuh ya dawo kotu

Yanzu-Yanzu: Bayan ya zame hanunsa daga sharia'r a jiya, lauyan Olisa Metuh ya dawo kotu

Mr. Emeka Otiaba (SAN), lauya mai kare tsohon mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Olisa Metuh ya sake bayyana a kotu a safiyar Talata sa'o'i 24 bayan ya sanar da cewa ba zai cigaba da kare Olisa Metuh ba.

Duk da cewa Metuh wanda ya yanke jiki ya fadi a kotu ranar Litinin bai samu hallartan shari'ar a ranar Talatan ba, Etiba ya bayyana kuma ya shaidawa kotu cewa shine lauya mai kare tsohon mai magana da yawun jami'iyyar PDP Olisa Metuh.

Etiaba ya zame hannunsa daga sharia'ar ne a ranar Litinin bayan alkalin kotun ya ce umurci a cigaba da sauraron karar Olisah Metuh duk da sumar da ya yi a kotun.

Yanzu-Yanzu: Bayan ya zame hanunsa daga sharia'r a jiya, Lauyan Olisa Metuh ya dawo kotu

Yanzu-Yanzu: Bayan ya zame hanunsa daga sharia'r a jiya, Lauyan Olisa Metuh ya dawo kotu

KU KARANTA: Kwanaki 4 da shigansa kurkuku, Sanata Jang ya biya dukkan bashin kudin lantarki da ake bin gidan yarin

Alkalin, Justice Okon Abang ya ce a cigaba da sauraron karar ne inda ya ce yanke jiki da faduwa da Metuh ya yi dabara ce kawai na batawa kotu lokaci da tsawaita shari'ar.

Etiaba ya ki amsa tambayoyin da alkalin ya masa a ranar Litinin din inda ya ce ya janye hanunsa daga shari'ar duk da cewa alkalin bai bashi izinin janye hanunsa daga shari'ar ba.

Alkalin ya bayyana cewa halayen da Etiaba ya nuna a kotun rashin da'a ne.

Duk ada hakan alkalin ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar Talata bayan likitocin kotun sun tabbatar da cewa Metuh yana bukatar ganin likita.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel