2019: Ka shirya shan kashi – PDP ga Buhari

2019: Ka shirya shan kashi – PDP ga Buhari

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya shirya shan kashi a zaben 2019, inda yayi ikirarin cewa dukkan alamu sun nuna cewa yan Najeriya basa yin shi kuma.

A jawabin da jam’iyyar ta fitar ta hannun kakakinta, Kola Ologbondiyan tayi ikirarin cewa Buhari bai cika alkawaran zabe da ya dauka ba, a cewarsu lamarin ya kai ga kasar ta shiga halin talauci da yunwa.

“Hakan na daga cikin gazawarsa wajen kyautatawa al’umman kasar, sannan kuma ya gaza yin wani aiki na azo a gani a ko wani yanki na kasar haka kuma bai cika ko kadan daga alkawarin da ya dauka lokacin yakin neman zaben 2015 ba.

2019: Ka shirya shan kashi – PDP ga Buhari

2019: Ka shirya shan kashi – PDP ga Buhari
Source: Twitter

"A yau masu jefa kuri’a sun kwana da sanin cewa Buhari da APC mayaudara ne. Bincikenmu ma ya nuna cewa shugaba Buhari bai taba tunanin cika ko wani alkawari nasa ba.

KU KARANTA KUMA: Sanata Ndume yayi kaca-kaca da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

“Babu shakka al’umman kasarmu dama kasarmu basu taba shiga irin wannan hali na kunci ba tun lokacin yancin kai a 1960, cewar jawabin."

A halin da ake ciki, mun samu labari cewa Sanatan Borno ta Kudu Ali Ndume ya je gidan Talabijin na Channels TV yayi kaca-kaca da Majalisar Dattawa karkashin Bukola Saraki da wasu ‘Yan tsirarrun Sanatocin Kasar

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel