Dakarun soji sun halaka makiyaya 25 a jihar Benue - Hukumar Tsaro

Dakarun soji sun halaka makiyaya 25 a jihar Benue - Hukumar Tsaro

Hukumar tsaro na kasa da ke Abuja ta sanar da cewa dakurun sojin Najeriya sun bindige makiyaya 25 har lahira a kananan hukumomin Gwer, Logo da Guma a yayin wani arangama da sukayi a ranar Asabar a jihar Benue.

Hukumar sojin ta ce an kashe makiyayan ne ta hanyar yi musu luguden wuta da jirgi mai saukan angulu kirar Mi - 35.

Sanarwan da kuma ce makiyayan sun kashe soja guda daya yayinda wasu biyu suka jikkata a yayin arangamar.

Dakarun soji sun halaka makiyaya 25 a jihar Benue - Hukumar Tsaro

Dakarun soji sun halaka makiyaya 25 a jihar Benue - Hukumar Tsaro

KU KARANTA: Kwanaki 4 da shigansa kurkuku, Sanata Jang ya biya dukkan bashin kudin lantarki da ake bin gidan yarin

Jami'in yada labarai na hukumar, Brig Janar John Agim ya tabbatar ta afkuwar lamarin ya ce sojojin suna gudanar da atisayen Operation Whirl Stroke ne a jihohin Benue, Nasarawa, Taraba da Zamfara lokacin da su kayi karo da makiyayan a Benue.

Agim kuma ya ce akwai wani soja guda daya da har yanzu ba'a gano shi ba bayan arangamar da akayi da makiyayan a Benue.

Ya cigaba da cewa cikin ayyukan da hukumar keyi wajen kawar da tsagera a kananan hukumomin Gwer ta yamma, Logo da Guma, dakarun sun hadu da dandazon makiyaya dauke da makamai kusa da kauyen Chetarer. Sojin sunyi musu luguden wuta da jirgin Mi-35

A kuma karshen makon da ya wuce, dakarun sojin sunyi wa wasu 'yan bindiga kwantar bauna inda suka kashe guda kuma suka kama wani makiyayi mai suna Adamu Abdullahi a Rukubi da ke karamar hukumar Doma na jihar Nasarawa.

Mai magana da yawun sojan ya ce za'a mika Abdullahi da sauran wadanda ake zargi ga yan sanda domin cigaba da gudanar da bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel