Kwanaki 4 da shigansa kurkuku, Sanata Jang ya biya dukkan bashin kudin lantarki da ake bin gidan yarin

Kwanaki 4 da shigansa kurkuku, Sanata Jang ya biya dukkan bashin kudin lantarki da ake bin gidan yarin

- Rahotanni sun ce Sanata Jang ya biya dukkan bashin kudin wutan lanatarki da ake bi gidan yarin Jos

- An dai jefa Sanatan a gidan yarin ne a ranar Laraba 16 ga watan Mayu

- Ana tuhumarsa ne da laifin karkatar da kudi N6.3 biliyan yayin da ya ke mulki a matsayin gwamnan jihar Filato

An ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Filato kuma Sanata mai wakiltan yankin arewacin Filato, Jonah David Jang ya biya dukkan bashin kudin lanatarki da ake bin gidan kurkukun Jos inda ake garkame shi tun ranar Laraba 16 ga watan Mayu.

An jefa Janga a kurkukun ne bayan hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasan ta'anati (EFCC) ta gurfanar da shi gaban wata babban kotu da ke jihar Kogi.

Kwanaki 4 da shigansa kurkuku, Sanata Jang ya yi wa gidan yarin sha tara na arziki

Kwanaki 4 da shigansa kurkuku, Sanata Jang ya yi wa gidan yarin sha tara na arziki

KU KARANTA: Yadda zaka kare kanka daga wasu cututuka 6 da ke adabar mutane lokacin damina

Ana tuhumar Sanatan ne da laifuka guda 12 wanda suke da alaka da cin hanci da almubazarranci da dukiyar al'umma wanda ta kai N6.3 biliyan yayin da ya ke mulki a matsayin gwamnan jihar Filato.

Jang ya umurci hadiminsa su biya dukkan bashin kudin wutan lantarki da ake bin gidan yarin ne bayan ya tarar da duhu yayin da ake jefa shi a kurkukun.

Daily Trust ta ruwaito cewa mai magana da yawun tsohon gwamnan, Clinton Garuba ya tabbatar da biyan kudin lantarkin inda ya kara da cewa Jang ya kuma biya wa wani fursuna mai fama da ciwon kafa kudin magani a asibitin koyarwa na Jos (JUTH).

Garuba ya ce: "Sanatan ya yi wa'azi a ranar Lahadi da ta gabata a gidan yarin inda ya ce yana cikin yanayi mai kyau kuma yana samun daman ganawa da likitocinsa."

Jami'in hulda da jama'a na gidan yarin bai yi tsokaci kan lamarin ba har yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel