Sanata Ndume yayi kaca-kaca da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Sanata Ndume yayi kaca-kaca da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

- Sanatan Kudancin Borno yayi watsa-watsa da Shugaban Majalisar Dattawa

- Majalisar Dattawan ta koma tamkar gidan Saraki da Dino Melaye inji Ndume

- Sanata Ali Ndume yace Bukola Saraki dai ya dauki kan sa wani Uban gidan su

Mun samu labari cewa Sanatan Borno ta Kudu Ali Ndume ya je gidan Talabijin na Channels TV yayi kaca-kaca da Majalisar Dattawa karkashin Bukola Saraki da wasu ‘Yan tsirarrun Sanatocin Kasar.

Sanata Ndume yayi kaca-kaca da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Ali Ndume ya soki shugabancin Bukola Saraki a Majalisa

Sanata Ali Ndume da ake hira da shi a Talabijin yace Bukola Saraki ya ci mutuncin Majalisar Kasar. Sanatan yace a baya su na tare da Shugaban Majalisar Bukola Saraki kafin abubuwa su juya ya ci amanar sa saboda kurum ya tsayawa gaskiya.

Ali Ndume na APC ya nuna cewa idan ta kama zai fede biri har wutsuya don kuwa Saraki yanzu ya dauki kan sa wani Uban-gidan Sanatocin ba Shugaban Majalisar ba. Sanatan yace Saraki ya dauki Majalisar kamar gidan sa shi da Dino Melaye.

KU KARANTA: Wani 'Dan Majalisa ya fara nuna cewa akwai badakala a kasafin bana

Ndume yace a kan yayi magana game da rantsar da Shugaban EFCC Ibrahim Magu da maganar shigo da motoci da kuma batun takardun makarantar Sanata Dino Melaye aka tsige shi daga matsayin sa kuma aka dakatar da shi daga Majalisa kwanakin baya.

A baya dai an dakatar da Sanatan na APC wanda yace sam ba a bi dokar kasa ba. Kuma dama jiya kun ji cewa ba mamaki a makon nan Majalisar Dattawan ta kara dakatar da Sanata Ali Ndume da kuma Sanata Ovie Omo-Agege da zarar an gama binciken su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel